Babbar Magana Yayin da EFCC Ta Kama Wani Matashin da Yace Shine Shugaban EFCC

Babbar Magana Yayin da EFCC Ta Kama Wani Matashin da Yace Shine Shugaban EFCC

  • Hukumar EFCC ta kama shugabanta na bogi a wani otal na babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata 14 ga watan Faburairu, 2023
  • Hukumar ta ce, an kama Salman Umar Hudu bayan da ya cuci wani mutum kudi N100,000 tare da ikrarin warware matsaloli
  • Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike don tabbatar da gaskiya da kuma gurfanar da mutumin mai shekaru 38

FCT, Abuja - Wani mutum ya shiga hannun hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya bisa laifin sajewa da yin ikrarin shine shugaban hukumar.

Wannan batu dai na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar a shafinta na Facebook, inda ta bayyana yadda ta yi caraf ta kama mutumin.

A cewar EFCC, ta kama Salman Umar Hudu a ranar Talata 14 ga watan Faburairu, 2023 a wani otal na Abuja, bayan samun bayanan abin da yake aikatawa.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

An kama Abdulrasheed Bawa na bogi a Abuja
Babbar Magana Yayin da EFCC Ta Kama Wani Matashin da Yace Shine Shugaban EFCC | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya fara da kuma matakin da EFCC ta dauka

A cewar hukumar, Salman dan shekaru 38 ne kuma dan asalin jihar Kano, kuma ya shiga hannun jami’ai bayan gano barnar da yake aikatawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa, Salman na gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar ta EFCC Abdulrasheed Bawa da dama dai gabatar da kansa a matsayin sauran jami’ai na hukumar na daban.

Da aka bincika, an gano Salman ya damfari wani mutum sama da N100,000 ta hanyar nuna masa zai warware masa wata matsala mai alaka da EFCC.

An ce an samu cikakkun bayanai da za su taimaka wajen gurfanar da Salman, kuma za a kai shi gaban shari’a bayan kammala cikakken bincike.

Ba wannan ne karon farko ba, an kama wani jami’in EFCC na bogi

A wani labarin na daban a shekarar da ta gabata, hukumar ta EFCC ta kama wani mutumin da ke ikrarin shi jami’inta ne, inda ya damfara mutane makudan kudade masu ban mamaki.

Kara karanta wannan

Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, an kwamushe Ume Ifechukwu Clinton a wani gida bayan da aka samu bayanai a kansa da abin da yake aikatawa na damfarar mutane babu gaira babu dalili.

Rahotanni sun bayyana cewa, Clinton ya yi amfani da sunan EFCC wajen yiwa wata mata tallan Crypto, inda ya damfare ta makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel