Ka’idar Musayar Kudi Ta CBN Za Ta Iya Shafar Zaben Bana, Jami’in INEC Ya Yi Gargadi Mai Daukar Hankali

Ka’idar Musayar Kudi Ta CBN Za Ta Iya Shafar Zaben Bana, Jami’in INEC Ya Yi Gargadi Mai Daukar Hankali

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a baya ta ce babu abin da zai taba zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba
  • Wani jami’in hukumar zabe ya ce shirin musayar kudi na CBN zai iya shafar zaben 2023, ya bayyana dalilai
  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar karancin kudi, suna kokawa kan halin da ake ciki a yanzu, musamman a bankuna

FCT, Abuja - Daya daga cikin kwamishinonin INEC a Abuja, Yahaya Bello ya ce akwai yiwuwar a samu tsaiko a zaben 2023 duba da yadda sabbin ka’idojin babban bankin Najeriya na takaita rike tsabar kudi, The Nation ta ruwaito.

Ya yi magana ne kan wannan lamarin yayin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki na Arewa ta Tsakiya game da zaben bata da kungiyar farar hula ta Centre for Transparency Advocacy (CTA) ta shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

Zabe zai iya tabuwa saboda karancin Naira
Ka’idar Musayar Kudi Ta CBN Za Ta Iya Shafar Zaben Bana, Jami’in INEC Ya Yi Gargadi Mai Daukar Hankali | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Kudurin CBN na sauya N200, N500 da N1000 ya zo da tsaiko da karancin kudi a hannun jama’a, ‘yan Najeriya sun gaza samun sabbin kudaden da aka buga.

Ana bukatar kudin jigilar kayan zabe

Bello ya ce, hukumar zabe na bukatar kudi don yin jigilar kayayyaki da kuma kula da harkar tsaro, inda yace karancin sabbin kudin zai iya shafar hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, matukar ba a yi wani abu ba, INEC a Abuja da sauran jihohi za su sha wahala wajen tura ma’aikatan zabe inda ya dace a zaben bana.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, baya ga kalubalen kudi, hukumar bata da wasu matsaloli, domin ta shirya sama da kaso 80% na abubuwan da take bukata a zaben na bana.

Dalilin da yasa kudi zai iya shafar zaben bana

Kara karanta wannan

Alkawari kaya ne: Tinubu ya fadi abu 1 da zai yiwa ASUU kowa ma ya huta idan ya gaji Buhari

Da yake bayani, ya ce:

“Kafin ranar zabe, muna bukatar tura masu gudanar da aikin.
“A daren ranar Juma’a (jajiberin zabe) a FCT, muna da ma’aikatan wucin gadi 12,000 da za mu ba tsabar kudi. Babu daga cikinsu da zai karbi ceki ko tiransifa. Ina magana ne ga FCT (12,000) da zai bukaci N5,000 a ranar Juma’a.
“Haka nan wadanda za su yi jigilar mutanenmu, makayyaki da ba da tsaro a rumfunan zabe za su bukaci kudi a hannu don yin haka. A Kano, muna da kananan hukumomi 44, kuma za su yi tafiya zuwa rumfunan zabe nawa ne.
“Akwai kudin tsaro saboda ba yadda za a yi a dauki jami’in tsaro a ajiye a rumfar zabe ba tare da ba shi kudin abinci ba kuma bana ganin N1000 da za a bashi zai tafi POS don cirewa.”

‘Yan Najeriya na ci gaba da kuka kan karancin kudi, CBN ya ce zai hukunta masu POS da ke karbar sama da N200 a hannun jama’a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ya dage karar gwamnoni 12 da CBN kan batun wa'adin tsoffin kudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel