Abin da Atiku Ya Ce Mani Zai Yi wa Nnamdi Kanu a Kwana 100 na Farko a Ofis - Wabara

Abin da Atiku Ya Ce Mani Zai Yi wa Nnamdi Kanu a Kwana 100 na Farko a Ofis - Wabara

  • A cikin watan Satumban shekarar nan, Mazi Nnamdi Kanu zai iya fitowa daga inda yake tsare
  • Shugaban majalisar amintattu na PDP ya ce Atiku Abubakar ya yi alkawarin fito da Nnamdi Kanu
  • Adolphus Wabara ya fadawa mutanen Umuahia shugaban IPOB zai samu ‘yanci idan aka zabi PDP

Abia - Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban majalisar amintattu a PDP, Adolphus Wabara ya nuna za a iya fito da Mazi Nnamdi Kanu.

Vanguard ta rahoto Sanata Adolphus Wabara yana cewa Atiku Abubakar ya ba shi tabbacin cewa shugaban ‘Yan IPOB zai samu ‘yanci a gwamnatinsa.

A cikin kwanaki 100 na farko da Atiku Abubakar zai yi a ofis idan ya zama shugaban kasa, zai saki Nnamdi Kanu ba tare da yanke masa wani sharadi ba.

Adolphus Wabara ya shaidawa Duniya wannan ne yayin da ya ke tallata ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP a wajen kamfe a garin Umuahia.

Kara karanta wannan

PDP 2023: Matsala Ta Kunno, Atiku Ya Soke Gangamin Kamfe a Jihar Wike Kan Abu 1

Za a daina cin tuwo babu Ibo - Wabara

Tsohon shugaban majalisar ya ce maganar a maida Ibo saniyar ware a Najeriya, zai zama tarihi da Wazirin Adamawa ya shiga fadar Aso Rock.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan an bar wajen kamfe, Sanata Wabara ya zanta da Vanguard, ya ce Atiku ba zai fasa cika alkawarinsa na ba shugaban kungiyar IPOB ‘yanci ba.

Atiku
Atiku da Ifeanyi Okowa a Abia Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

Bisa dukkan alamu Wabara ya yarda da Atiku, ya ce ‘dan takaran jajirtaccen mutum ne wanda yake cika alkawari, kuma bai jin tsoron wani mahaluki.

Channels ta ce a wajen kamfe, sabon shugaban majalisar ta BOT a babbar jam’iyyar hamayyar ya fadawa magoya bayansu Atiku ne wanda ake bukata.

Domin karkato da hankalin jama’a, ‘dan siyasar ya ce Atiku zai hada-kan al’umma, sannan a shawo kan matsalolin yau irinsu canza fasalin kasa.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

"Abin farin cikin ga Ndigbo shi ne, Atiku Abubakar zai saki yaronmu ba tare da wani sharadi ba a cikin kwana 100 na farko a ofis.
Mutum ne mai cika alkawari, zai yi abubuwan da suka dace. Shi ne mai ceton da ake bukata a a yau. Mai son Najeriya ya zabi PDP."

EFCC da Gwamnatin Kogi

An ji labari Kwamishinan labarai na Kogi, Kingsley Fanwo ya ce Hukumar EFCC ta na karyar zargin wasu iyalan Gwamna Yahaya Bello da rashin gaskiya.

A wani jawabi da ya fitar, an ji Kingsley Fanwo ya ce EFCC ta na cafke na-kusa da Gwamna ba tare da an gayyace su ko an samu umarnin Alkalin kotu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel