Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

  • Hadimin ‘Dan takaran Shugaban kasa a PDP, Phrank Shaibu ya yi wani raddi ga Femi Fani-Kayode
  • Kwanan nan Cif Femi Fani-Kayode ya zargi Atiku Abubakar da yin zama da wasu Janar a gidan soja
  • ‘Dan siyasar ya ce Atiku yana neman kawowa zaben 2023 cikas, zargin da ‘dan takarar ya musanya

Abuja - ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga DSS, ‘yan sanda da sauransu, su kama Femi Fani-Kayode.

The Guardian ta rahoto cewa Alhaji Atiku Abubakar ya fitar da wannan jawabi ne ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin sadarwa, Phrank Shaibu.

Phrank Shaibu ya fitar da jawabi na musamman a ranar Lahadi a matsayin raddi ga wasu maganganu masu nauyi da Femi Fani-Kayode ya yi a shafinsa.

Da yake magana a dandalin Twitter, Fani-Kayode wanda Darekta ne a kwamitin neman zaben Bola Tinubu, ya ce ana shirye-shiryen juyin mulki.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Zargin kifar da Gwamnatin farar hula

Tsohon Ministan tarayyar ya zargi Atiku Abubakar da wasu manyan Janar na sojoji da nufin kifar da gwamnati ko kuma su hana yin zabe a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto Shaibu yana mai cewa tun farko ba su yi niyyar maidawa jigon na APC martani ba domin a ‘yan shekarun nan, ya yi suna a sharara karya.

Atiku
Atiku Abubakar da 'Yan PDP a Abia
Asali: Facebook

Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar na PDP ya ce sai da ta kai kungiyar ‘yan jarida ta NUJ tayi Allah-wadai da Fani-Kayode saboda irin abin kunyarsa.

Zargin ba na wasa ba ne - Atiku PCC

"Amma bai kamata ayi wasa da zargi da rade-radin shirya juyin mulki ba, domin cin amanar kasa ce wanda hukuncin aikata shi, shi ne kisa.
A yayin da muke jinjinawa sojojia watsi da karyar Fani-Kayode, mu na kira ga sauran jami’an tsaro su gayyace shi domin ya yi karin bayani."

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Daily Trust ta rahoto Shaibu yana cewa ‘dan siyasar ya yi wa mutane da yawa sharri, a dalilin haka ya kamata hukuma ta dauki matakin da ya dace kan shi.

Shaibu ya ce ya kamata DSS tayi masa yadda tayi wa Marigayi Obadiah Mailafia, sannan ya tunawa ‘Yan Najeriya an taba zargin FFK da shan kwaoyoyi.

Naka sai naka

An ji labari Kashim Shettima ya soki Atiku Abubakar, ya ce bai taimaki Arewa a lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasar Najeriya ba.

Shettima yake cewa ‘naka na ka ne’, amma nakan da ya san cewa shi na ka ne, shi ne na ka, ya ce wanda aljihunsa kurum ya sani, to ba na ka ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel