Gwamna Yana So a Garkame Shugaban EFCC da Ya Taso Matarsa da ‘Danuwansa a Gaba

Gwamna Yana So a Garkame Shugaban EFCC da Ya Taso Matarsa da ‘Danuwansa a Gaba

  • Gwamnatin jihar Kogi ta maida martani a kan cafke mai dakin Gwamna tare da wasu mutane
  • Kingsley Fanwo ya zargi hukumar EFCC da biyewa ‘Yan adawa wajen kunyata Yahaya Bello
  • Kwamishinan Jihar ya ce babu kudin da suka bace daga baitul-malin Kogi kamar yadda ake zargi

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta zargi hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya da biyewa abokan gaban siyasarsu domin cin ma burinsu.

A rahoton The Cable, an ji Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya fitar da jawabi yana rokon a kama Shugaban EFCC.

Mista Kingsley Fanwo ya bukaci Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya da ya kama Abdulrasheed Bawa, a daure shi a gidan yari yadda aka yi umarni.

Kwamishinan labaran yake cewa abin takaici ne a ce hukumar da ya kamata ta maida hankali wajen yakar rashin gaskiya, ta buge da biyewa ‘yan adawa.

Kara karanta wannan

Tsoffin Kudi: Gwamna Masari Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Bankuna Da Yan Kasuwa a Jihar Katsina

Ana so a batawa Gwamna suna

Fanwo yake cewa EFCC ta dage wajen ganin an bata sunan Gwamna da gwamnatin jihar Kogi. Labarin nan ya fito a jaridar Independent ta ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin abin da yake faruwa, Fanwo ya ce jami’an EFCC sun maida ‘yan jarida sun zama Alkalai, ya kara da cewa babu abin da zai dauke hankalin Gwamna.

Gwamnan Kogi
Gwamna Yahaya Bello tare da Rasheeda Bello Hoto: www.armadanews.com
Asali: UGC
"Sabon yunkurin EFCC shi ne zargin wasu daga iyalan Gwamna da rashin gaskiya, ana cafke su ba tare da an gayyace su ko da umarnin kotu ba.
Kuma duk da akwai umarnin kotun da ta haramta masu gurfanar da su uwa gaban Alkali.
Wannan lamarin ya kara fito da rashin bin doka da saba ka’idar aiki da kuma gidadancin da ake yi a hukumar yaki da rashin gaskiyar kasar.
Abin da suka yi a karshe ya nunawa ‘Yan Najeriya su na da mugun nufi a kan Gwamna da Gwamnatin jihar Kogi, jama’a kuma sun gane su."

Kara karanta wannan

Da Gaske Matasa Sun Yi Wa Gwamna Buni Ruwan Duwatsu? Gwamnatin Yobe Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

- Kingsley Fanwo

Gwamnatin Kogi ta ce babu kudin da suka bace daga baitul mali, don haka bai kamata a bari Bawa ya cigaba da aiki a matsayin shugaban EFCC ba.

Hukuncin daure Bawa

A makon da ya gabata wata kotu da ke Kogi ta bada umarnin a tsare Abdulrasheed Bawa a gidan gyaran hali da ke Kuje a babban birnin tarayya a Abuja.

Kwanaki kadan da zartar da wannan hukunci, sai hukumar EFCC ta sake gurfanar da mai dakin Gwamnan Kogi, Rasheeda Bello da wasu mutanen a kotu.

Rahoto ya nuna daga cikin wadanda ake zargi tare da mai dakin Gwamnan akwai Ali Bello. Ana tuhumarsu agaban Alkali da aikata laifuffuka fiye da 18.

Asali: Legit.ng

Online view pixel