Shekaru 25 na Bata: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Yayi Auren Sirri, Ya Bar ta

Shekaru 25 na Bata: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Yayi Auren Sirri, Ya Bar ta

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta yi fallasa ga wani saurayi a soshiyal midiya wanda tayi ikirarin yayi mata alkawarin aure
  • Budurwar da zuciyarta ke cike da kudna, ta wallafa hotuna a shafinta na Facebook kuma ta dinga zuba zagi kan saurayin kan cin amanarta
  • Martani daban-daban sun biyo bayan wannan wallafar da tayi a shafinta inda wasu suke ta caccakarta yayin da wasu ke goyon bayanta

Wata budurwa 'yan Najeriya mai suna Chinesa Emmanuel, ta fallasa saurayin da ya bar ta tare da auren wata ta daban.

Budurwar cike da kunar zuciya ta dinga wurga tsinuwa ga tsohon saurayinta kuma ta sanar masa cewa ya aureta ko kuma ba zai ga kwanciyar hankali a gidansa ba.

Cin amanar budurwa
Shekaru 25 na Bata: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Yayi Auren Sirri, Ya Bar ta. Hoto daga @Chinesa Emmanule
Asali: Facebook

A yayin martani ga wallafar, wasu jama'a sun yi ikirarin cewa budurwar ta dauka nauyin karatunsa a kasar waje tare da bashi muhimman shekaru 25 na rayuwarta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar Aure ta Fita da ATM din Mijinta, Tayi Waddaka da Kudinsa Son Ranta

Budurwar mai cike da kunar rai da bakin ciki ta wallafa hakan a shafinta na Facebook.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ikenna Nworah lokaci yayi da za ka sallame ni ko kuma ka rasa jin dadi, zaman lafiya da farin ciki a auren nan.
"Ikenna Nworah za ka ji miyagun labarai da safe kuma za ka yi aikin banza sannan za ka rasa komai.
"Ikenna Nworah so ka ke ka gudu amma karya ka ke, babu inda za ka je. Ikenna Nworah zo ka fadawa Zion cewa ka yi alkawarin aure na kuma ka sanar da cewa ka sallame ni. Ka zo ka sallame ni ko ka ganni a gidan ka yau."

Soshiyal midiya tayi martani

Ulasi Uche yace:

"Zo ka ga labarin shekaru 25. Kawai a saka shi a kwalba a jefa a rafi."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da tankar ta fadi ta fashe, hukumar ta bayyana halin da ake ciki

Mercy Atu tace:

"Haba matan nan , ta yaya za ki soyayya da namiji tsawon shekaru 25? Haaa, shekara daya tak ni ba zan yi da mutum ba. Mijina mun hadu mun yi soyayyar wata shida kuma a yau mun yi aure muna zaman lafiya, za mu yi shekara 25 a shekara mai zuwa. Shawarata gare ki, ki yi hakuri ki cigaba da rayuwa."

Ofure Alex yace:

"A gaskiya na tausaya mata. Na duba shafinta na Facebook kuma a bayyane yake cewa tana ta fama. Allah ya kawo miki sauki."

Prince Maduabuchi yayi stokaci da:

"Wadanda basu san mene ne soyayya ba, zasu ga laifin budurwar. Soyayya sadaukarwa ce, ba ta damu ko ka samu abinda kake so ko a'a ba. Ku ga laifin malalacin mutumin wanda ya cuceta."

Mata Aure ta haifa yaro da IUD a hannunsa

A wani labari na daban, wata matar aure ta fallasa yadda ta haifa jinjiri rike da IUD a hannunsa duk da tsarin iyalin da tayi.

Tace sun yi aure da mijinta amma basu shirya haihuwa ba, hakan yasa ta saka IUD don gujewa haihuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel