Tashin Hankali Yayin da Tankar Mai Ta Fashe a Kan Titin Ore Zuwa Benin a Jihar Ondo

Tashin Hankali Yayin da Tankar Mai Ta Fashe a Kan Titin Ore Zuwa Benin a Jihar Ondo

  • An samu tashin hankali yayin da wata tankar mai dauke da kaya ta fashe, ta kama da wuta a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ba a samu asarar rai ba, kuma ana ci gaba da kokarin kashe gobarar da ta tashi
  • Hukumar kiyaye haddura ta bayyana cewa, ta tura jami’anta zuwa wurin, ta kuma ba masu motoci shawari

Ore, jihar Ondo - Rahoton da muke samu daga jihar Ondo a ranar Laraba 8 ga watan Faburairu na cewa, wata tankar mai ta fadi a kan babban titin Ore-Benin a karamar hukumar Odigbo ta jihar, Punch ta ruwaito.

Wannan ne karo na biyu da irin mummunan hadarin ke aukuwa a yankin a cikin kwanaki tara, inda a baya wata ranar 31 ga watan Janairu wata tankar kananzir ta kama da wuta ta kone direban kurmus.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana Wahalar Layin Mai, Babban Abu Ya Fashe a Gidan Man Fetur

Kwamandan yankin a hukumar kiyaye haddura ta kasa, Mr. Sikiru Alonge ya tabbatar da faruwar lamarin.

Motar mai ta fashe a Ondo
Tashin Hankali Yayin da Tankar Mai Ta Fashe a Kan Titin Ore Zuwa Benin a Jihar Ondo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, direban tankar ya kubuta, kuma ba a samu asarar rai daga wannan mummuna hadari da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya daura alhalin irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da wasu direbobin motocin da ke kaiwa ga fashewar tayoyin mota, rahoton Guardian.

Ana shawo kan lamarin

Alonge ya kuma bayyana cewa, ana ci gaba da kokari don ganin kashe wutar, kuma jami’an hukumar ta FRSC sun dura wurin domin daidaita cunkoso.

A cewarsa:

“Hadarin ya faru ne saboda fashewar taya. Wannan ya sa tankar ta karkace sannan ta zubar da abin da ta dauko wanda ya kai ga tashin wuta, daga baya kuma sai fashewa mai karfi.
“Babu asarar rai daga wannan al’amarin. Muna hada kai da hukumar kashe gobara a Ondo don taimakawa wajen kashe wutar, tunda babu ofishin kashe gobara a Ore.

Kara karanta wannan

Ma'aikaciyar da ke Zuwa Aiki a Kasa Kullum ta Tsinta N6.908m, Ta Kai Cigiya An Samu Masu Kudin

“Mun tura jami’anmu zuwa yankin don dakile cunkoso da cikowa a wurin.”

Ya kuma shawarci masu motoci da su ke maida hankali ga tuki tare da tabbatar da sun bi ka’ida da dokar tuki.

Rahotonmu na baya ya bayyana yadda wani abu ya fashe a wani gidan man jihar Ondo a kwanakin baya da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel