Matar Aure ta Haifo Jariri Rike da Abun Tsarin Iyali Bayan ta Daure Mahaifa Kada ta Haihu

Matar Aure ta Haifo Jariri Rike da Abun Tsarin Iyali Bayan ta Daure Mahaifa Kada ta Haihu

  • Wata mata mai shekaru 20, Violet Quick da mijinta John Francis sun gano da yadda suke shirin tarbar 'dan su na farko duk da tsarin iyalin da suka yi
  • Sai dai, an ga yadda jinjirin nasu ya zo duniya dauke da maganin tsarin iyalin da mahaifiyarsa ta dauki watanni da rufe mata kofar mahaifarta da shi
  • Matar ta bayyana yadda ta yi fama da laulayi wanda hakan ya janyo hankalinta don yin gwajin juna biyu inda aka tabbatar ma ta da hakan

Wata mata mai shekaru 20 da ta samu juna biyu yayin da ta ke amfani da maganin hana haihuwa ta haifo wani jinjiri wanda ya shigo duniya dauke da abinda tadon rufe mahaifa da shi tsarin iyali a hannunshi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kawo hujja: 'Yan sanda sun karya tsohon gwamna Matawalle kan zargin sun masa sata a gida

Matar aure
Matar Aure ta Haifo Rike da Abun Tsarin Iyali Bayan ta Daure Mahaifa Kada ta Haihu. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Violet Quick, daga Idaho, ta auri mijinta John Francis tana da shekaru 19, inda basu shirya zama iyaye ba, sai dai, shekara daya kacal da aurensu suka gane yadda suke dab da samun rabo.

Violet da John sun tarbi 'dan su na farko a duniya karshen watan Janairu, 2022, jaridar Daily Mail UK ta rahoto.

A wani bidiyo da ke tashe, wanda ya bar miliyoyin jama'a baki bude, sabuwar mahaifiyar ta wallafa bidiyon yadda 'dan su ya ke kankame da na'urar tsarin iyalin a lokacin da aka haife shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta labarta yadda Rudy ba bar hatta ma'aikatan jinyar cikin mamaki yayin da suka garzayo don ganin wa idanuwansu maganin tsarin iyalina hannun jinjirin.

"Yayin da duk ma'aikatan jinyar suka yi ido biyu da jinjirin da maganin tsarin iyalin sun sha mamaki."

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

- Violet ta yi tsokaci kan bidiyon.

A bidiyo daban-daban, Violet ta bayyana yadda ta yanke shawarar yin gwajin juna biyun saboda tana yawan amai tsawon makonni biyu.

Kamar yadda ta rubuta:

"Na dauki tsawon watanni tara ina amfani da maganin hana daukar ciki kafin in samu juna biyu, kuma dalilin da yasa na yanke shawarar yin gwajin juna biyun shi ne yadda nake yawan jin amai tsawon makonni biyu, kuma ina yin aman akai -akai.
"Ban san mai ke faruwa ba, hakan yasa na yi gwajin wanda ya tabbatar min da ina dauke da juna biyu."

Ta shawarci mabiyanta da su yi gwajin idan suna fuskantar irin wani daga cikin abubuwan da ta fuskanta, ko da kuwa sun yi tsarin iyali.

An yi imani da cewa na'urar tsarin iyalin (IUD) na taka rawar gani wurin hana daukar ciki da kashi 99. Duk da haka, mata da dama sun dauki juna biyu yayin amfani da shi.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Bayyana Yadda Aurensu Da Tsohon Mijinta Ya Mutu Cikin Watanni 7 Kacal

Magidanci ya kama matarsa da gardi a Otal, ya fashe da kuka

A wani labari na daban, wani magidanci ya karyarwa da masu kallon bidiyonsa zuciya bayan ya fashe da kuka sakamakon kama matarsa da yayi da gari a otal.

Yayi yunkurin kaiwa ga namijin da ya ya gani tare da matarsa, amma matar ta hana tare da nuna bata nadama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel