Abinda Matata Tayi: Magidanci Ya Bayyana Waddakar da Matarsa Tayi da Kudinsa Bayan ta Dauka ATM dinsa

Abinda Matata Tayi: Magidanci Ya Bayyana Waddakar da Matarsa Tayi da Kudinsa Bayan ta Dauka ATM dinsa

  • Wani 'dan Najeriya magidanci ya je soshiyal midiya inda ya nuna mamakinsa kan kayayyakin da matarsa ta siya da ATM dinsa
  • Matarsa ta fita inda tace tana son siyo balan-balan saboda wani bidiyo da zasu yi tare da shi amma ta kare da cin karenta babu babbaka
  • Yayin da ta dawo, ya leka jakarta inda ya ganta makare da kayayyakin bukata kamar mayonnaise, soson yara da sauransu

Wani magidanci 'dan Najeriya ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamni ta TikTok inda ya bayyana halaka kudinsa da matarsa tayi.

A wani bidiyon TikTok, yace za su yi wani bidiyo ne da ita amma take son siyo balan-balan domin hakan.

Matar aure
Abinda Matata Tayi: Magidanci Ya Bayyana Waddakar da Matarsa Tayi da Kudinsa Bayan ta Dauka ATM dinsa. Hoto daga @bennyomoedo
Asali: TikTok

Yace ta sanar masa cewa mintuna biyar kacal za ta dauka amma sai da ta kwashe mintuna goma.

Yayin jiranta, ya dinga jin fitar kudi daga asusun bankinsa kuma ya gane cewa tayi amfani da kudinsa wurin kashe gararin gabanta.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Bidiyon Wata Yar Najeriya Da Ta Jera Tafiya Da Wasu Zakuna 2 Ya Dauka Hankali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abun dariyan shi ne yadda mijin ya toge a hanyar shiga gidan tare da tuhumar matarsa kan kashe kudinta da lokacin da ta bata.

Matar daga bisani ta shiga cikin gidan kuma ta fito da balan-balan din, mayonnaise, soson jarirai da sauran kayayyakin da ta siyo.

Ta bashi hakuri kan yawan abubuwan da ta siyo duk da bata tambayesa ba kuma ta nemi gafarar mijinta.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi martani

ChrisRex11 tace:

"Sak abinda mata ta take yi, duk ranar da ta ke son fita siyayya, tsoro nake ji saboda za ta siyo abubuwan da har a gida muke da su."

Atasaana tace:

"Tayi nasara duk da haka, wa ya ga murmushin da ke fuskarsa zuwa karshen bidiyon. Fushin duk ya tsere bayan ta taba shi."

ladyk tace:

"Murmushi kawai nake yi yayin da nake kallon wannan bidiyon. Yadda Ubangiji ya halicce mu daban ne."

Kara karanta wannan

Kada Ku Kashe Ni, Zan Tona Asiri: Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Ta Zauce, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

Ijeoma I. tace:

"Kada ka damu, za a sake samu wasu kudin. Mata ya cancanci su zama cikin farin ciki."

Courage tace:

"Me yasa wasu ma'auratan ke gwada mana kamar aure bashi da dadi, zan yi aure Asabar mai zuwa, ina gayyatar kowa."

Abun mamaki: Matar aure ta haihu duk da tsarin iyali

A wani labari na daban, wata matar aure ta haifo santalelen jariri duk da tsarin iyalin da take yi da IUD.

Ta sanar da cewa, jaririnta ya fito da IUD din a hannunsa, lamarin da ya ba jama'a masu yawa mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel