Labarin Yadda Basaraken Arewa ya Nada Bola Tinubu a Matsayin ‘Jagaban’ a 2006

Labarin Yadda Basaraken Arewa ya Nada Bola Tinubu a Matsayin ‘Jagaban’ a 2006

  • Shekaru kusan 17 da suka wuce Asiwaju Bola Tinubu ya zama Jagaban a masarautar Borgu
  • Marigayi Halliru Dantoro Kitoro III ya ba Gwamnan Jihar Legas wannan sarauta da ya zama Sarki
  • Halliru Dantoro Kitoro III ya hadu da ‘dan siyasar ne a lokacin da suka je majalisar dattawa a 1992

Abuja - A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta dauko salsala da tarihin zaman Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Jagaban na masarautar kasar Borgu.

Marigayi Mai martaba Halliru Dantoro Kitoro III shi ne wanda ya ba Asiwaju Bola Tinubu wannan sarauta ta Jagaban a lokacin yana Sarkin Borgo.

A wajen nadin sarautar, mujallar City People ta rahoto Halliru Dantoro Kitoro III a shekarar 2006 yana bayanin dacewar Bola Tinubu da Jagaban.

A yayin da Basaraken ya ba Tinubu sarautar Jagaban, ya zabi Mai dakinsa, uwargidar gwamnan Legas a lokacin (Remi Tinubu) ta zama Yun Bana.

Kara karanta wannan

Jerin Wadanda Suka Halarci Zaman Majalisar Magabata Ranar Juma'a

Tsohuwar alaka mai tarihi

Mai Borgu ya shaida cewa abokantakarsa da Gwamnan jihar Legas na lokacin ta yi tsawon shekaru 24, ta samo asali tun lokacin su na majalisa a 1992.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jamhuriyya ta uku, Bola Tinubu da Halliru Dantoro Kitoro suka lashe zabe, suka zama Sanatoci a majalisar dattawa, kafin zuwan Janar Sani Abacha.

An zabi Tinubu ne a matsayin Sanatan yankin Legas ta yamma a jam’iyyar SDP, saishi kuma Dantoro ya lashe zaben Arewacin Neja a karkashin NRC.

Tinubu
Dakaren Birnin Gwari, Bola Tinubu Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Duk da ba mu jam’iyya daya, ni da Tinubu mun fahimci mun yi tarayya a harkokin kasa da-dama, sai mu da wasu ‘yan kishin kasa muka fara tafiya tare.
A cikin sauki sai muka samu kusanci da juna, amma ba mu san kasar mu za ta shiga mawuyacin yanayi ba. A 1993, Sani Abacha ya dawo da mulkin soja.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Rudani, Mambobin PDP 8,000 Sun Koma APC a Arewa

Mai martaban yake cewa shi da wasu Sanatoci 35 irinsu Tinubu, Chuba Okadigbo, Abu Ibrahim suka fara kalubalantar kifar da gwamnatin da soja suka yi.

Halayen kirkin da Mai Borgu ya gani

Sarkin Borgu ya ce ya gano ‘dan siyasar yana iya sadaukar da ransa kan gaskiya, hakan ta sa da ya samu sarauta, ya tuna da abokin gwagwarmayarsa.

Vanguard ta ce sarautar Jagaban ta na nufin jagoran jarumai a kasar Arewa maso tsakiyar Najeriyan. An yi nadin sarautar a ranar 26 ga Fubrairu 2006.

A Oktoban 2015 Sarkin ya rasu, Tinubu yana cikin wadanda suka yi masa ganin karshe.

Ana hasashen bogi - Kwankwaso

Ana yawan yin hasashen LP ce za ta lashe zabe mai zuwa. An ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya ce idan hasashen gaskiya, Jam’iyyar NNPP ce a kan gaba.

‘Dan takaran yana jin tsoron magoya bayan Peter Obi su jawo tashin hankali idan suka sha kasa a zabe mai zuwa saboda burin da suka ci daga hasashen nan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Atiku, Tambuwal Ya Yi Wa Tinubu Kyakkyawar Tarba a Sokoto

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel