Jerin Wadanda Suka Halarci Zaman Majalisar Magabata Ranar Juma'a

Jerin Wadanda Suka Halarci Zaman Majalisar Magabata Ranar Juma'a

Shugaba Muhammadu Buhari a yau Jum'a ya jagoranci zaman majalisar magabata da dukkan masu ruwa da tsaki na kasa domin tattaunawa kan abubuwa biyu da suka shafi Najeriya.

Majalisar ta tattauna kan lamarin zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni.

An ji ta bakin shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, kan shin ya shiryawa zaben?

Farfesa Mahmoud ya ce lallai shirye suke, a cewar Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.

Aso ROck
Jerin Wadanda Suka Halarci Zaman Majalisar Magabata Ranar Juma'a Hoto: Aso Rock
Asali: Facebook

A bangaren Sifeto Janar na yan sanda kuwa, an tambayesa shin wani irin shiri suke don tabbatar da tsaro lokacin zaben.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Malami, IGP Alkali ya ce suma shirya suke.

Game da lamarin Naira kuwa, mambobin majalisar sun ce ba yu adawa da sauya fasalin Naira amma gwamnan CBN ya buga isassun sabbin kudi ko kuma ya fito da tsaffi mutane suyi amfani.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muna Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Da Sharadi 1: Majalisar Magabata

Ga jerin wadanda suka halarci wannan zama

Wadanda suka halarta a mutum:

 1. Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Yakubu Gowon
 2. Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar
 3. Tsohon shugaban kasan Goodluck Jonathan
 4. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
 5. Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan;
 6. Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila
 7. Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna
 8. Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba
 9. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos
 10. Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno
 11. Ministan birnin tarayya, Mohammed Bello;
 12. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha;
 13. Antoni Janar kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami
 14. Gwamnan bankin CBN Godwin Emefiele
 15. Shugaban hukumar INEC, Mahmoud Yakubu
 16. Hafsun Sojin dake wajen:
 17. Shugaban hafsun tsaro, Janar Lucky Irabor
 18. Shugaban hafsun sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya
 19. Shugaban hafsun sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo
 20. Shugaban hafsun sojin sama, AVM Ishiaka Amao
 21. Sauran hukumomin tsaro:
 22. IGP na yan sanda, Baba Usman Alkali
 23. Kwamandan NSCDC, Dr Ahmed Abubakar Audi
 24. Tsohon Shugaban Alkalan tarayya, Belgore
 25. Tsohon Shugaban Alkalan tarayya, Mahmud Muhammad
 26. Shugaban ma'aikatar gwamnati, Yemi Esan

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Obasanjo, Jonathan, Abdussalam, Gwamnoni Sun Hallara Don Taron Majalisar Magabata

Wadanda suka halarta ta yanar gizo:

 1. Tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Olusegun Obasanjo
 2. Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun
 3. Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa
 4. Gwamna Yahaya Bello na Kogi
 5. Gwamna Atiku Bagudu (Kebbi),
 6. Gwamna Dapo Abiodun (Ogun),
 7. Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto
 8. Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Plateau
 9. Mataimakin gwamnan Nasarawa
 10. Mataimakin gwamnan Bauchi

Asali: Legit.ng

Online view pixel