Jirgin Super Tucano Ya Yiwa Yan Ta'addan Boko Haram Kimainin 100 Ruwan Wuta

Jirgin Super Tucano Ya Yiwa Yan Ta'addan Boko Haram Kimainin 100 Ruwan Wuta

  • Jami'an tsaron Najeriya sun sake samun gagarumin nasara a yankin Arewa maso gabas
  • Masanin harkokin tsaro a tafkin Chadi yace yanzu haka yan ta'addan na yabawa aya zaki
  • A makon da ya gabata, ana rigima tsakanin yan ta'addan ISWAP da na Boko Haram kuma sun kashe juna

Jirgin yakin Super Tucano ta yi sanadiyar mutuwar gomman yan ta'addan Boko Haram yayinda suke zaman ganawa a cikin dajin Sambisa, jihar Borno.

Wannan hari na zuwa ne bayan tsawon mako guda ana artabu tsakanin yan ta'addan Boko Haram da yan ta'addan ISWAP inda suka hallaka juna.

Tucano
Jirgin Super Tucano Ya Yiwa Yan Ta'addan Boko Haram Kimainin 100 Ruwan Wuta Hoto: NAF
Asali: UGC

Zagazola Makama, masani harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya bayyana cewa majiyoyi sun larburta yadda sojoji suka kai wannan hari ranar 10 ga Febrairu a Gaizuwa, karamar hukumar Bama ta jihar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin sun bayyana cewa hukumar Soji ta tira jiragen Super Tucano 2 dake karkashin atisayen Operation Hadin Kai bayan samun labarin leken asiri cewa yan ta'adan Boko Haram na ganawa.

A cewar Zagazola, sojojin na isa wajen suka ga sama da yan ta'adda 100 da gomman babura.

Yace an hallaka da dama cikinsu yayinda saura suka tsallake rijiya da baya.

Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

A wan labarin daban, Tsohon Ministan Neja Delta kuma dan takaran gwamnan jihar Cross Rivers karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Usani Usani Uguru, ya tsallake rijiya da baya.

Wasu yan bindiga sun budewa motarsa wuta a babban titin Calabar-Ikom.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a harin.

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

Mr Usani na hanyarsa ta zuwa mahaifarsa ne, garin Nko, dake karamar hukumar Yakurr ta jihar tare da dan takarar mataimakin gwamnan jihar.

Kwamishanan yan sandan jihar, Sule Balarabe, ya tabbatar da labarin harin.

Ya bayyana cewa an kai musu harin ne ranar Juma'a misalin karfe 4 tsakanin karamar hukumar Akamkpa da Biase.

Yace wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suke budewa motar Ministan kirar Ford mai lamba AAA 41 AQ inda mutum biyu suka rasa rayukansu.

Kwamishanan ya ce an yi garkuwa da mutum uku cikin motar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel