Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

  • Yankin kudancin Najeriya ya yi kaurin suna da kaiwa yan takarar siyasa harin kisa
  • An kaiwa Gwamnan Anambra hari, an kaiwa Sanata Uba hari, an kaiwa dna takarar gwamnan Ebonyi, yanzu kuma tsohon ministan Buhari
  • Hadimin dan takaran ya ce da kyar suka tsallake rijiya da baya kuma an yi garkuwa da wasu

Tsohon Ministan Neja Delta kuma dan takaran gwamnan jihar Cross Rivers karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Usani Usani Uguru, ya tsallake rijiya da baya.

Wasu yan bindiga sun budewa motarsa wuta a babban titin Calabar-Ikom.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a harin.

Mr Usani na hanyarsa ta zuwa mahaifarsa ne, garin Nko, dake karamar hukumar Yakurr ta jihar tare da dan takarar mataimakin gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

Usani
Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamishanan yan sandan jihar, Sule Balarabe, ya tabbatar da labarin harin.

Ya bayyana cewa an kai musu harin ne ranar Juma'a misalin karfe 4 tsakanin karamar hukumar Akamkpa da Biase.

Yace wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suke budewa motar Ministan kirar Ford mai lamba AAA 41 AQ inda mutum biyu suka rasa rayukansu.

Kwamishanan ya ce an yi garkuwa da mutum uku cikin motar.

A jawabinsa:

"Motar da aka budewa wuta aka kashe mutum biyu na dauke da mutum 7 ciki har da yan sanda biyu, ASP Ibor Bassey da Insfekta Ebro Ebri, wadanda suka arce sannan suka kira ofishin hukuma."
"Da wuri aka tura jami'ai wajen kuma kawo yanzu sun ceto mutum uku."

Kwamishanan ya ce wadanda aka ceto mambobin jam'iyyar PRP ne da suke tare da tsohon Minista.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

Mai magana da yawun tsohon ministan, David Agabi, ya ce da baya suka tsallake rijiya a harin.

Yan Bindiga Sun Kaiwa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Hari An Kashe Direbansa

A jiya, mun kawo muku cewa dan takarar kujerar gwamnan jihar Ebonyi karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Farfesa Bernard Odo, ya tsallake rijiya da baya bayan mumunan harin da aka kai masa.

Direbansa dai bai yi sa'a ba, sun kashe shi har lahira yayinda sauran dogaransa suka samu rauni munana

Asali: Legit.ng

Online view pixel