Malaman Jami’o’i Dole Ne Su Rantse Ba Za Su Nuna Bambanci Ba a Aikin Zabe, Inji Hukumar INEC

Malaman Jami’o’i Dole Ne Su Rantse Ba Za Su Nuna Bambanci Ba a Aikin Zabe, Inji Hukumar INEC

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ya ce, akwai bukatar malaman jami'a su rantse kafin kama aikin zaben bana
  • Ya bayyana hakan ne a gaban shugabannin malaman jami'an a wata tattaunawa da ya yi dasu a ranar Alhamis
  • Ana ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa, hukumar INEC ta ce tabbas za a yi zabe

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce dole ne malaman jami'o'in da za su yi aiki a matsayin turawan zaben bana su yi rantsuwar ba za su nuna bambanci wajen tattara sakamakon zabe ba.

Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu yayin wani taro tsakaninsa da shugabannin jami'o'i da ya gudana a ranar Alhamis, 9 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Adam Zango Ya Fallasa Sirrin Aurensa, Yace Zai Rabu da Matarsa, Ya Sanar da Dalilai

A cewarsa, rantsuwar za ta kasance ne kan kowane ma'aikacin zabe kamar yadda sashe na 26 na kundin zaben 2022 ya tanada.

INEC ta ce dole malaman jami'a su rantse za su yi gaskiya
Malaman Jami’o’i Dole Ne Su Rantse Ba Za Su Nuna Bambanci Ba a Aikin Zabe, Inji Hukumar INEC | Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Wadanda ba za a bari su yi aikin zabe ba

Yakubu ya ce hukumar ba za ta yi aiki da malamin jami'an da alakarsa da siyasa ta bayyana karara ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Dole na yi gargadin cewa duk ma'aikacin da ke kati ko kuma yake harkar siyasa ba za a tantance shi ba.
"Har ila yau, wadanda basa siyasa amma aka san suna da alaka da siyasa su ma ba za a tantance su ba. Bugu da kari, wadanda aka taba kamawa da badakalar zabe ma ba sa ciki."

A samar da kwararru masana makamar aiki

A nasa bangare, shugaban hukumar jami'o'i ta Najeriya (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed ya bukaci malaman jami'o'in da za a tura aikin zaben su kasance kwararru wajen sauke nauyin da aka daura musu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Za Mu Yi Idan Yan Daba Suka Sace Na'urar BVAS", INEC

Hakazalika, shugaban kwamitin shugabannin jami'o'i, Farfesa Lilian Salami ya ba da tabbacin cewa, wadanda za a tantance daga malaman jami'an za su kasance kwararru.

Ya kara da cewa, za a tabbatar zakulo masu kamun kai wadanda za su sauke hakkin da aka daura musu ba tare da wata tangarda ba.

An rufe jami'o'in Najeriya a shirin zabe

Idan baku manta ba, hukumomi a Najeriya sun bukaci a rufe dukkan jami'o'i domin gudanar da aikin zabe cikin tsanaki, Punch ta ruwaito.

A irin wannan yanayi, sarkin Musulmi ya ce ba zai tsoma kansa a lamarin siyasa ba, sai dai zai yiwa kasa addu'ar samun shugaba na gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel