Zaben 2023: "Abin Da Za Mu Yi Idan Yan Daba Suka Sace Na'urar BVAS", INEC

Zaben 2023: "Abin Da Za Mu Yi Idan Yan Daba Suka Sace Na'urar BVAS", INEC

  • INEC tana da dabarar da za ta yi amfani da shi don yin maganin yan daban siyasa da ke shirin sace na'urar BVAS yayin babban zabe
  • Hukumar zaben mai zaman kanta, a ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa idan yan daba sun sace na'urar za su kashe daga ofishinsu
  • Hukumar ta kara da cewa idan an sace na'urar ko kuma an kai su wani wurin domin yin wani manakisa, jami'in zabe a rumfar zai sanar da hukumar

Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta bayyana matakin da za ta dauka idan yan daban siyasa sun kai wa ma'aikatanta hari sun sace na'urar Bimodal Voter Registration Systems (BVAS) yayin babban zabe.

Yayin wani hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, mataimakin direktan watsa labarai na INEC, Lawrence Bayode, ya ce za a kashe na'urar ta BVAS daga ofis idan hakan ya faru.

Kara karanta wannan

Karancin Naira Da fetur: Shugaban INEC Ya Fadi Matsayarsa Game Da Yiwuwar Samun Matsala a Zaben Bana

Shugaban INEC
Zaben 2023: "Abin Da Za Mu Yi Idan Yan Daba Suka Sace BVAS", INEC.
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayode ya ce za a dauki wannan matakin ta yadda bata garin da suka sace ba za su iya sauya kuri'u ba.

Ya ce:

"Idan aka sace BVAS, muna da tsarin yadda za a kashe wannan na'uarar ta BVAS.
"Za mu kashe ta yadda duk wanda ya sace na'urar ba zai iya komai da shi ba domin na'urar na tura bayanai da aka tabbatar ne da kansa ko da ba a latsa ba. Idan an bar shi da kansa, zai tura sakamako zuwa matattara."

A hirar wanda ita ma Punch ta yi nazari, Bayode ya bayyana cewa idan barayi sun sace na'uarar sun kai ta wani wuri da nufin yin manakisa, jami'in zabe na rumfar zai tura rahoto.

Ya ce:

"Idan irin hakan ya faru, jami'in rumfar zabe zai sanar kuma za a kashe wannan na'urar daga ainihin babban na'ura ta yadda ba za a iya komai da shi ba."

Kara karanta wannan

Hanzari ba gudu ba: Jega ya fadi manyan kalubale biyu na zaben 2023, ya shafi kowa a Najeriya

Zaben 2023: Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Masu Zabe Su Sani Game Da BVAS

A yayin da ake tunkarar babban zaben Najeriya a watan Fabrairun 2023, mutane da dama sun kosa lokacin ya yi domin su tafi su sauke nauyin da kasa ta dora musu.

Wani sabon abu kuma shine sabuwar na'urar yin zabe na BVAS da INEC ta kawo domin inganta nagartar zaben tare da hana yin magudi.

Sai dai akwai wasu muhimman abubuwa dangane da na'urar da ya kamata mutane su sani kafin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel