Sanatan APC Ya Fadi Wanda Zai Zama Babban Kalubale Wajen Shirya Zaben 2023

Sanatan APC Ya Fadi Wanda Zai Zama Babban Kalubale Wajen Shirya Zaben 2023

  • Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya soki tsarin canza wasu kudi da Gwamnan CBN ya fito da shi
  • ‘Dan majalisar tarayyar ya ce da farko an yi tunanin bankin CBN zai yi maganin masu boye kudi ne
  • A halin yanzu, Sanata Bamidele yana ganin babban banki zai hana abubuwa su tafi sumul a zabe

Abuja - Shugaban kwamitin shari’a da hakkin bil Adama a majalisar dattawa, Michael Opeyemi Bamidele ya zargi CBN da neman kawo cikas.

Ganin yadda aka sauya takardun kudi ba tare da an wadata da sabbin kudin ba, Daily Trust ta rahoto Sanata Michael Opeyemi Bamidele yana babatu.

Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya yi wannan bayani a wajen wani taro da kwamitinsu ya shirya a majalisa kan dokar zabe na shekarar 2022.

Kwamitiocin majalisar wakilan tarayya da na dattawa sun kira zama domin mutane su tattaima a kan sabuwar dokar da aka yi wa garambawul a bara.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta Tsaida Lokacin da Za Ayi wa Ma’aikata Sabon Karin Albashi a Najeriya

Sai CBN sun yi gyara - Sanata

‘Dan majalisar wanda yana cikin ‘yan kwamitin harkar zabe ya ce tsarin da babban banki na CBN ya fito da shi wajen cire kudi, ba mai bullewa ba ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Guardian ta ce Sanata na Ekiti ya nuna akwai bukatar majalisar tarayya ta sake yin aiki a kan dokar zabe domin a gyara inda aka samu matsaloli.

Sanata
Majalisar Dattawa Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

“Da farko CBN sun fada mana ana harin manyan da suka tara kudi, suka boye biliyoyi a cikin masai ne. Mun yi tunanin mutanen nan ake hari.
Yanzu mun gani cewa talaka da yake kan titi ne ake yaka. Mutane su na kwana a bankuna saboda ba za su iya cire ‘yan kudin da suka mallaka ba.
Dole mu fahimci harkar siyasar tattalin arzikin sha’anin zabe. Mu na cewa ne INEC ba za ta iya yin aikinta ba sai da gudumuwar bankin CBN?

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

Idan ‘yan sanda suka samu matsala wajen kai-komo, su ma za su ruga neman agajin CBN ne?
Mu na yaki da Boko Haram, idan sojoji suka rasa kudi a bankunansu, su ma za su je wajen bankin CBN ne domin samun tallafi na musamman?
Halin da ake ciki kenan, kuma a matsayin masu ruwa da tsaki, bankin CBN ne babban barazana ga wadannan zabukan da ake shirin gudanarwa.”

- Michael Opeyemi Bamidele

Mun yi shirin zabe - APC

APC ta ce ta shiryawa babban zabe, kuma tana sa ran dinbin ‘Yan Najeriya za su sake kada mata kuri’a a zaben kwarai wanda yake cikin zaman lafiya.

Rahoton ya ce a daidai wannan lokaci, APC ta zargi ‘yan adawa da yaudara da sharri da karya wajen kamfe, Felix Morka ya fadi haka a wani jawabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel