Gwamnati ta Tsaida Lokacin da Za Ayi wa Ma’aikata Sabon Karin Albashi a Najeriya

Gwamnati ta Tsaida Lokacin da Za Ayi wa Ma’aikata Sabon Karin Albashi a Najeriya

  • Dr. Chris Ngige yi ya yi alkawarin gwamnatin tarayya za tayi karin albashi nan da Mayun 2024
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa ya sanar da hakan a wajen wani taron NLC
  • Ngige ya yi gargadi, ya ce a guji neman gwamnati ta biya bukatun ma’aikata da karfi da yaji

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a Najeriya, Chris Ngige ya ce an kammala duk wasu shirye-shirye na karin albashin ma’aikata.

Rahoto daga Daily Trust ya zo a ranar Laraba cewa Chris Ngige ya shaidawa jama’a, gwamnatin tarayya za ta fito da sabon tsari na biyan ma’aikata.

Ministan ya ce za ayi wannan ne nan da watan Mayun shekarar 2024 ko kafin zuwa lokacin.

Dr. Chris Ngige ya kuma ja-kunnen kungiyoyin ‘yan kwadago da su guji yi wa gwamnati katslandan, su na neman tursasa abin da suke so ayi.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

NLC tayi taro a Abuja

Mai girma Ministan ya yi wannan jawabi ne da aka gayyace shi zuwa wajen taron kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen taron da aka yi ranar Talata ne Ministan tarayyar ya gargadi mahalartan cewa su na sabawa dokar kwadago da ta wajabta kwas a MINILS.

Buhari
Muhammadu Buhari ya sa hannu a kasafin kudi Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Tsohon Gwamnan na Anambra yake cewa kafin mutum ya zama shugaba a kungiyoyin kwadago yanzu, sai ya yi kwas a wannan makaranta.

Rahoton ya ce yin karatun zai taimakawa shugabannin wajen fahimtar tsarin aiki.

A jawabin da ya gabatar, Ngige ya yi kira ga kungiyar NLC da ta tabbatar da cewa Gwamnonin jihohin kasar nan sun dabbaka dokar ECA ta 2010.

Wannan doka ta ba ma’aikata damar samun diyya yayin da suka samu rauni ko suka mutu a wurin aiki.

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

Babban bako, Farfesa Yemi Osinbajo

This Day ta ce Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo shi ne babban bako a taron, ya yi magana kan abubuwan da suka shafi aiki.

Yemi Osinbajo ya yi kira ga ma’aikatan kasar da su kara kokari duk da irin kalubalen da suke fuskanta na karancin albashi da makamantansu a aiki.

Majalisar koli za ta zauna

A wani rahoto da aka samu a safiyar nan, an ji shugaba Muhammadu Buhari zai zauna da duka tsofaffin shugabannin kasa domin samun mafita.

Za a gayyaci Gwamnan CBN, Shugaban INEC da Sufetan ‘Yan Sanda domin jin shirin zabe. Tsofaffin CJN da Gwamnonin jihohi za su halarci zaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng