Za Ki Sha Bakar Wahala – Wata Uwa Ta Tsinewa Diyarta Da Ta Yi Aure Ba Tare Da Saninta Ba

Za Ki Sha Bakar Wahala – Wata Uwa Ta Tsinewa Diyarta Da Ta Yi Aure Ba Tare Da Saninta Ba

  • Wata uwa yar Najeriya ta tsinewa diyarta wacce ta yi aure cikin sirri a jihar Enugu ba tare da ta sanar da ita ba
  • Matar wacce ta yi magana cikin kunar rai ta ce ta dauki dawainiyar makarantar yarinyar tata amma ta yi watsi da ita a lokacin aurenta
  • Ta kuma ce diyar tata za ta sha bakar wahala a rayuwa tunda ta yi aure ba tare da ta gayyace ta ba

Wata mata yar Najeriya ta fito bainar jama'a ta tsinewa diyarta wacce ta yi aure ba tare da ta gayyace ta ba.

Fusatacciyar uwar ta ce ta sha wahalar haihuwar diyarta mai suna Chinyere amma ta yi watsi da ita a ranar aurenta.

Uwa, diyarta da angonta
Za Ki Sha Bakar Wahala – Wata Uwa Ta Tsinewa Diyarta Da Ta Yi Aure Ba Tare Da Saninta Ba Hoto: Twitter/@instablog9ja.
Asali: Twitter

A cewar matar, ba a gayyace ta ba haka kuma ba a sanar da ita batun auren ba wanda ya gudana a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

“Na San Yadda Yake Ji": Budurwa Ta Jizga Saurayinta a Bainar Jama’a, Ta Karbe Wayar Da Ta Siya Masa a Bidiyo

Bidiyon wata uwa tana tsinewa 'yarta

Mahaifiyar ta yi magana da kakkausar lafazi a cikin wani bidiyo da ya yadu wanda shafin @instablog9ja ya wallafa. Ta bayyana yadda ta yi wahalar haihuwar Chinyere da kuma saka ta a makaranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda basu gayyaceta ko sanar da ita batun auren ba, matar ta ce Chinyere da mijinta za su sha bakar wahala a rayuwa.

An wallafa hotunan auren Chinyere tare da bidiyon. An gano malamai suna hada aurenta da mijinta a bidiyon wanda ya yadu kuma ya haifar da martani a Twitter.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Merit78914812 ta ce:

"Allah zai kawo mafita. Wasu za su sanya maki albarka."

@OluwaMozey ya yi martani:

"Ainahin dalilin da yasa bata sanar da ke ba kafin ta aikata."

@Qriscero ta yi martani:

Kara karanta wannan

"Na Taki Sa'ar NYSC": Budurwa Mafi Gajarta Za Ta Auri Dan Bautar Kasa Mafi Tsawo A Sansaninsu, Hotunansu Sun Yadu

"Mata da bakin zuciya! Kada ki ji tsoro, Chinyera."

@LivinTroller ta ce:

"Akwai dalilai da dama da zai sa uwa ta tsinewa diyarta. Amma babu daga ciki da ya isa hujja mai kyau. A bangaren diyar kuma, ko me uwarki ta aikata maki, cin mutuncinta haka bai isa dalili ba."

Ango ya yi biris da amarya a wajen shagalin bikinsu, ya mayar da hankali kan wayarsa

A wani labarin kuma, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wani ango da ya wancakalar da lamuran amaryarsa ya mayar da hankalinsa kacokan a kan wayarsa a yayin da ake liyafar bikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel