Karancin Mai Da Kudi: An Kashe Mutum Daya Yayin da Ake Karo Tsakanin Yan Sanda da Bata-Gari a Ibadan

Karancin Mai Da Kudi: An Kashe Mutum Daya Yayin da Ake Karo Tsakanin Yan Sanda da Bata-Gari a Ibadan

  • An zub da jini yayin zanga-zanga kan karancin kudi da man fetur a garin Ibadan lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya
  • An bindige mamacin yayin arangama tsakanin bata-gari da jami'an yan sanda a mararrabar kasuwar Apata
  • Kakakin yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ce yan daban sun kaddamar hare-hare kan jami'an wadanda suka rasa zabi da ya wuce daukar mataki

Oyo - Zanga-zanga kan karancin man fetur da Naira ya yi sanadiyar rasa ran mutum daya a Ibadan, babban jihar Oyo.

An kashe mutumin wanda ya kasance mamba a kungiyar yan sa-kai a ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairu, a yankin Apata da ke Ibadan yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zaton yan daba ne.

Zanga-zanga
Karancin Mai Da Kudi: An Kashe Mutum Daya Yayin da Ake Karo Tsakanin Yan Sanda da Bata-Gari a Ibadan Hoto: @Ibadantwitta
Asali: Twitter

Adewale Osifeso, kakakin yan sandan jihar, ya bayyana cewa wasu yan daba sun farmaki jami'an tsaro yayin da suke fatrol a wajajen mararrabar kasuwar Apata, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Ta'adda Suka Kashe Yansakai 41 A Harin Kwanton Bauna A Dajin Katsina

Wani bangare na jawabin na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wani lamari mai ban mamaki, yan daban wadanda suka shirya da kyau don cin zalin mazauna da cin zarafin masu shaguna, da sace kayayyakinsu sun farmaki jami'an tsaron hadin gwiwa a lokacin da suka hangi ayarin motocinsu inda suka bude masu wuta, suna ta jefe-jefen duwatsu, wukake da muggan makamai."

Nan take jami'an tsaron suka shiga aiki sannan suka dakile lamarin daidai da tsarin aikin yan sanda kamar yadda Osifeso ya bayyana.

Kakakin yan sandan ya kara da cewar an dauki gawar marigayin da ya rasa ransa a arangamar zuwa wani asibitin gwamnati, jaridar The Cable ta rahoto.

Ana ci gaba da fuskantar karancin man fetur da Naira

Tun a ranar Juma'a, 3 ga watan Fabrairu, ake cikin fargaba a yankunan Ibadan yayin da mazauna ke zanga-zanga kan karancin man fetur da kudi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Ana fama da dogayen layi a akwatunan ATM yayin da yan Najeriya ke fafutukar samun sabbin kudi wanda suka yi wahala a wannan lokaci.

Yan Najeriya, musamman masu ababen hawa na shan wahala wajen samun man fetur daga gidajen mai yayin da gidajen mai da dama da yan bunburutu ke siyar da mai fiye da farashin da gwamnatin Najeriya ta yarda da shi.

ICPC sun kai samame banki, sun gano sabbin kudi a durowa

A wani labarin, a kokarinta na ganin sabbin naira sun wadata a kasar, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bazama aiki.

A cikin haka, ICPC ta bankado damin sabbin kudi da aka boye a cikin durowan wani banki bayan ta kai samame bankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel