Gimbiya Fatima: Bidiyo da Hotuna daga Shagalin Auren Diyar Sarkin Zazzau

Gimbiya Fatima: Bidiyo da Hotuna daga Shagalin Auren Diyar Sarkin Zazzau

  • Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya aurar da diyarsa Gimbiya Fatima Nuhu Bamalli a ranar Juma'a da ta gabata
  • Bikin Gimbiyar kuma 'yar gata ya samu halartar manyan mutane da suka hada da 'dan takarar gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani
  • Tabbas an yi shagali tare rakashewa a bikin kyakyawar gimbiyar wacce ta auri masoyinta Ahmed Audu Abubakar

Zaria, Kaduna - A ranar Juma'a, 3 ga watan Fabrairun 2023, Mar Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya aurar da diyarsa, Gimbiya Fatima Nuhu Bamalli.

Gimbiya Fatima
Gimbiya Fatima: Bidiyo da Hotuna daga Shagalin Auren Diyar Sarkin Zazzau. Hoto daga Sanata Uba Sani
Asali: Facebook

An daura auren ne a masallacin da ke fadar Sarkin a garin Zazzau inda manyan jama'a, 'yan siyasa da masu mulki suka halarta.

A daurin auren da aka yi bayan Sallar Juma'a, Sanata Uba Sani, 'dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam'iyyar APC, ya samu halarta.

Kara karanta wannan

Kaico: Dauda Ya Kashe Dan Uwansa Yayin Dambe Kan N1,000 A Legas

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fatima Bamalli
Gimbiya Fatima: Bidiyo da Hotuna daga Shagalin Auren Diyar Sarkin Zazzau. Hoto daga Aisha Bamalli
Asali: UGC

Gimbiya Fatima
Gimbiya Fatima: Bidiyo da Hotuna daga Shagalin Auren Diyar Sarkin Zazzau. Hoto daga Aisha Bamalli
Asali: UGC

Babu shakka bikin auren Gimbiya Fatima ya kasance na 'yar gata kuma jinin sarauta.

An fara shagalin bikin da saka lalle, kamu, aka yi dinne sannan aka rufe da budar kai cike da salo mai kayatarwa wanda ke nuna jinin sarauta da gata.

Manyan mawakan zamani da suka hada da fitaccen mawakin hausa, Ali Jita, ya gwangwaje amarya, ango, 'yan bikin da sauran jama'a da wakarsa.

An gan manyan mata da suka amsa sunayensu suna rausayawa tare da takun kasaita wanda isar su da izzarsu ta bayyana karara.

An kai Gimbiya Fatima Bamalli dakinta da angonta Ahmed Audu Abubakar. Allah ya basu zaman lafiya.

Abun mamaki: Matar aure ta haihu duk da tsarin iyalin da take yi

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Violet ta haifa santalelen yaron namiji bayan ta saka maganin tsarin iyali na IUD a jikinta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ku Amshi Kudinsu Amma Ku Zabe Ni, Peter Obi Ya Fada Wa Yan Najeriya

Babban abun mamakin shi ne yadda ta haifa yaron da IUD din a hannunsa rike, lamarin da ya birkita malam jinya da suka gani.

Violet ta sanar da cewa, basu shirya haihuwa ba koda suka yi aure da mijinta, hakan yasa suka yi tsaron iyali.

Ta saka IUD amma bayan wani lokaci ta fara amai tare da fama da zazzabi, hakan yasa tayi gwajin ciki kuma ta ga tana dauke da juna biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel