Karancin Naira: Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

Karancin Naira: Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

  • Fusatattun matasa sun rufe tituna da ofishohin gwamnati a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo
  • A faifan bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya an ji wata mata na cewa hakurin mutane fa ya kare
  • Matasa masu zanga-zanga sun rike kwalayen cewa za'a sake sabuwar tafiyar Endsars irin wacce akayi a 2020

Ibadan - Mumunar zanga-zanga ta barke a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo sakamakon halin kunci, tsadar kaya, da kuma rashin takardun Nairan siya a Najeriya.

Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda fusatattun matasa sun tare hanyoyi suna kone-konen tayoyi.

TheNation ta ruwaito cewa matasan sun kai hari ofishin gwamnan jihar, Seyi Makinde.

Har direbobin motocin haya ba'a bari a baya ba wajen zanga-zangar.

Kalli hotuna da bidiyoyin:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

Yan Najeriya fa sai dai kuyi hakuri, sauya fasalin kudin nan wajibi ne muyi shi: Ministar kudi

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed Shamsuna, ta yi kira da yan Najeriya su yi hakuri da wahalhalin da suke sha game da karancin kudi sakamakon sauya fasalin manyan takardun Naira.

Ministar ta bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.

Zainab ta ce wahalar za ta zo ta kare amma abinda gwamnatin ke yi shine daidai don gyara tattalin arzikin Najeriya.

A wani labarin daban, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi Allah sannan ta duba halin da talakawa suka shiga sakamakon sauya fasalin Naira.

Gwamnan wanda aka fi sani da Kauran Bauchi ya ce mutane basu tsira da wahala da tsadar man fetur ba, gashi yanzu ko kudin sayan man babu.

Kara karanta wannan

Karina Bayani: Gwamnonin APC Sun Roki Buhari Ya Bari a Dinga Amfani da Tsofaffi da Sabbin Kudi

Kaura ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel