Sauya Fasalin Naira a Wannan Lokacin Bai Ba da Ma’ana Ba, Cewar Gwamnan Kaduna El-Rufai

Sauya Fasalin Naira a Wannan Lokacin Bai Ba da Ma’ana Ba, Cewar Gwamnan Kaduna El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana gwamnatin Buhari ta sauya fasalin Naira a shekarun baya kuma aka samu nasara
  • Ya ce a wannan karon, gwamnatin bata yi sauyin a lokacin da ya dace ba, ya bayyana matsalar da ke tattare da hakan
  • Gwamnatin Buhari ta sauya fasalin Naira, ba kowa ne ya amince da batun sauyin ba, mutane da yawa suna guna-guni

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai a ranar Laraba ya caccaki batun sauya fasalin Naira, inda yace batun sam bai kama hankali na siyasa da tattalin arziki ba a daidai wannan lokacin.

Ya bayyana cewa, duk da manufar tana da kyau wajen cimma burin kawo sauyi a kasar, amma lokacin yin hakan da kuma wa’adin da aka saka ya saba lamba.

El-Rufai ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a wani shirin Channels Tv da Legit.ng Hausa ta sa ido a kai a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

El-Rufai ya yi tsokaci game da sabbin kudi
Sauya Fasalin Naira a Wannan Lokacin Bai Ba da Ma’ana Ba, Cewar Gwamnan Kaduna El-Rufai | Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

Da yake tsarkake shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya El-Rufai ya ce akwai wasu bara-gurbi da ke kokarin bata sunan shugaban da kuma kokarin ganin sun kawo tsaiko ga gwamnatinsa da jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba wannan ne karon farko da Buhari ya sauya fasalin Naira ba

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Buhari a farkon mulkinsa na soja ya sauya fasalin Naira ba tare da samun wata matsala ba.

“Misali na biyu da zan bayar shine na batun sauya fasalin kudi. Dole ka fahimci shugaban kasa. Mutane na ganin laifin gwamnan babban banki game da sauyin fasalin kudi, amma a’a.
“Dole ka yi waiwaye kuma ka duba baya a farkon mulkin Buhari (a matsayin shugaban soja). Ya yi wannan; gwamnatin Buhari-Idiagbon ta sauya fasalin kudi kuma sun yi cikin sirri da nufin kama wadanda suka sace kudi suka boye. Manufa ce mai kyau.

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

“Shugaban kasan na da ‘yanci. Amma yinsa a wannan lokacin a wani kayyadadden lokaci bai ba da ma’ana ta siyasa da tattalin arziki ba.”

A halin yanzu dai 'yan Najeriya na ci gaba da neman mafita game da batun sauyin fasalin Naira, wasu sun fara amfani da kudaden kasar Nijar don yin harkokin kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel