Ku Ajiye Kabilanci, Ku Zabi Mutumin Da Ya Cancanta, Kwankwaso Ya Shawarci Masu Zabe

Ku Ajiye Kabilanci, Ku Zabi Mutumin Da Ya Cancanta, Kwankwaso Ya Shawarci Masu Zabe

  • Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa na 2023, Rabiu Kwankwaso ya shawarci yan Najeriya kan wanda za su zaba
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya bukaci yan Najeriya da kada su yi zabe bisa kabilanci ko addini
  • Kwankwaso ya nemi masu kada kuri'u su zabi shugaba mai nagarta wanda ya cancanta.

Oyo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargadi yan Najeriya da kada su kuskura su yi zabe bisa la'akari da kabilanci ko addini.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya shawarci masu zabe da su zabi mutumin da ya cancanta kuma mai nagarta, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kwankwaso
Ku Ajiye Kabilanci, Ku Zabi Mutumin Da Zai Iya, Kwankwaso Ya Shawarci Masu Zabe Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso, wanda ya yi magana a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo yayin wani taro da kungiyar ci gaban kudu maso yamma ta shirya ya ce:

Kara karanta wannan

Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa

"Bai kamata al'ummar Najeriya su yi siyasar kabilanci da addini ba, ku zabi nagartattun shugabanni kawai."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wasu mutanen ma basu fahimci zahirin gaskiyar da ke kasa ba a yau. Kowani dan Najeriya na neman mafita ne. Babu wanda ke jiran makwabcinsa ko wani shugaba ya ce ga hanya.
"Duk dan takarar jam'iyyar da ya fake da sunan kabilanci ko lamuran da suka shafi addini, wannan jam'iyya ko dan takara a matakin kasa ya sha kaye a zaben tunma kafin a fara shi.
"Abun da yan Najeriya ke fadi shine wa zai iya kare kasar nan a bangaren rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da ababen more rayuwa da muke gani."

Ku zabe ni don cika muradinku, Kwankwaso ga yan Najeriya

Da yake sanar da cewar NNPP ta sabonta fatan yan Najeriya, Kwankwaso ya bayyana cewa wadanda suka fusata da halin da ake ciki na iya sauya labarin a 2023 ta hanyar zabarsa a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya

Kwankwaso ya yi alkawarin kawo karshen satar man fetur wanda ke yi wa tattalin arziki illa idan ya lashe zaben.

A rahoton Leadership, Kwankwaso ya ce shine ya fi cancanta da wannan aiki, inda ya ce aiki ne na ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciko ba wai batun kabilanci ko addini ba.

A wani labari na daban, kungiyar yakin neman zaben Obi-Datti ta yi watsi da rade-radin cewa dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi zai yi maja da takwaransa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel