An Yi Cacar Baki Tsakanin Gwamna Ortom da Sanusi Kan Mummunan Harin Bam Da Aka Kai a Nasarawa

An Yi Cacar Baki Tsakanin Gwamna Ortom da Sanusi Kan Mummunan Harin Bam Da Aka Kai a Nasarawa

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bukaci tsigaggen sarkin Kano, Sanusi, ya je ya ji da batun tsige shi da aka yi sannan ya bar shi ya shugabancin jiharsa
  • Ortom ya yi martani ga wani bidiyo da ke yawo inda tsohon sarkin ya koyar da shi yadda ake shugabanci sannan ya nemi ya yi koyi da takwaransa na jihar Filato
  • Gwamnan ya jaddada cewar majalisar dokokin jihar Benue ce ta kafa dokar hana kiwo a fili da basaraken ke magana a kanta

Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci tsohon sarkin Kano, Alhaji Lamido Sanusi da ya fuskanci shari’ar da ake yi da shi a kotu game da tsige shi da aka yi daga karagar mulki sannan ya kyale shi da jiharsa.

Babban sakataren gwamnan na Benue, Nathaniel Ikyur ya bayyana cewa ubangidan ya yi jawabin ne a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue da ke Makurdi yayin kaddamar da cibiyar DOHAPITU, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Atiku Ya Magantu A Kan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Yi Masa Kan Zargin Wawure Kudi

Sarki Sanusi da Gwamna Ortom
An Yi Cacar Baki Tsakanin Gwamna Ortom da Sanusi Kan Mummunan Harin Bam a Nasarawa Hoto: Samuel Ortom
Asali: Twitter

A rahoton wanda aka gabatar ga manema labarai a daren Talata, 31 ga watan Janairu, an ce Ortom na martani ne ga wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya inda tsohon sarkin yake koyar da gwamnan kan yadda ake shugabanci.

Ikyur ya ce Sanusi ya yi furuci a bidiyon inda yake danganta Ortom da lamarin tashin bam da ya afku a jihar Nasarawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu Fulani makiyaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan na Benue ya jaddada cewar har yanzu hukumomin da abun ya shafa suna nan suna gudanar da bincike a kan lamarin, rahoton Channels TV.

Sanarwar ta kuma yi zargin cewa tsigaggen sarkin ya bukaci Ortom da ya yi koyi da takwaransa na jihar Filato kan yadda ake kula da banbanci.

Babu ruwanka da abun da ya shafi jihata, Ortom ga Sanusi

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan APC Ya Maka ‘Dan Jam'iyyarsa a Kotu, Ya Ce Dole Ya Biya Shi N250m

A martaninsa, Ortom ya bukaci tsohon sarkin Kanon da ya daina shiga harkokin jiharsa, yana mai korafin cewan duk da tarin ilimi da wayewarsa, Sanusi ya koma yi masa bita da kulli don cimma kudirinsa.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Gwamnan ya ce yayin da ba shi da niyan yin cacar baki da tsigaggen sarkin saboda yadda yake daukar rayukan jama'a da muhimmanci, ya jaddada cewar majalisar dokokin jihar Benue ce ta kafa dokar hana kiwo a fili wanda dakataccen sarkin ke magana a kai a bidiyon kuma ita ta sanar da hukuncin da za a yankewa duk mutumin da ya take dokar.
"Ya ce gwamnatin jihar Benue ko gwamnan ba su da karfin ikon tura jirgi mara matuki ko wani kayan aikin soji kowani bangare na kasar.
"A lokacin da ya kamata, zan mayar da martani ga mugun furuci da aka yi a kaina ga shugaban kasa. Zan yi magana kan labarina sannan na fallasa mugun aikin d ake yi wa wadanda ake kallo a matsayin shugabanni masu ilimi da fada aji."

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Matashi Dan Najeriya Ya Dau Zafi, Ya Yi Barazanar Tarwatsa Banki Yayin da Jami’an Tsaro Suka Hana Shi Shiga a Bidiyo

Bam ya halaka mutane masu yawa a jihar Nasarawa

A baya mun ji cewa wani bam ya tashi a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa inda ya yi sanadiyar rasa rayukan Fulani da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel