Sanatoci Sun ba Ma’aikatar Isa Pantami Wa’adin Awa 48 a Fadi Inda Aka Kai N13.9bn

Sanatoci Sun ba Ma’aikatar Isa Pantami Wa’adin Awa 48 a Fadi Inda Aka Kai N13.9bn

  • ‘Yan Majalisar dattawa su na binciken Ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani, ma'aikatar Pantami
  • Binciken kwamitin Mathew Uroghide ya nuna AGF ya ba ma’aikatar N13.9bn a cikin shekaru biyar
  • Sanata Mathew Uroghide ya ce dole ma’aikatar tayi wa majalisa bayanin yadda aka yi da kudin

Abuja - Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta na da wa’adin awanni 48 domin tayi bayanin Naira biliyan 13.9 da ta karba tsakanin 2017 da 2021.

Punch ta ce shugaban kwamitin da ke kula da asusun gwamnati a majalisar dattawa, Sanata Mathew Uroghide ya ba ma’aikatar wa’adin nan a ranar Talata.

‘Yan majalisa sun yi wani zama a jiya a garin Abuja inda ake binciken inda wasu kudi su ka shiga.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta tarayya, William Alo ya gaza yi wa Sanatoci bayanin inda suka kai Naira biliyan 13.9.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Jawo Wanda Obasanjo, 'Yaradua Suka Dauko a Jiki, Ya Damka Masa Mukami

William Alo ya wakilci Ma'aikata

Gazawar William Alo a gaban kwamitin majalisar dattawan ya jawo Sanata Mathew Uroghide ya bada tsawon kwana biyu domin ma’aikatar ta iya wanke kan ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce Alo bai iya gabatar da wasu hujjoji da su gaskata shi ba, wannan abin ya ba kwamitin binciken majalisar mamakin yadda ake tafiyar da ma’aikatarsa.

Isa Pantami
Isa Pantami tare da Shugaban kasa Hoto; @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Yayin da ake tsakiyar bincike sai Sakataren din-din-din na ma’aikatar da Darektansa su ka bukaci majalisar kasar ta kara masu lokaci domin su kawo wasu takardu.

Wannan bukata da ma’aikatan suka gabatar ya fusata kwamitin Sanatocin domin kuwa an shafe fiye da watanni hudu ana neman yadda za ayi wannan zama da su.

Daily Post ta rahoto Uroghide ya ce bincikensu ya nuna masu Akanta Janar ya warewa ma’aikatar tarayyar N13.9bn domin yin wasu ayyuka daga 2017 zuwa 2021.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Gwamnan CBN Ya Tona Asiri Kan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Babban Laifin Bankuna

A dalilin haka kwamitin ya yi ta aikawa ma’aikatar wasika domin su yi bayani a kan kudin.

An ba ma'aikatar wa'adin kwana 2

"Sai kuma a yau ka zo tare da Darektan ma’aikatar, ku na neman karin lokacin da ba za a kara maku ya wuce ranar Alhamis na makon nan ba, domin dole kwamitin nan ya gabatar da rahotonsa ga majalisa kan yadda ma’aikatarku da sauran ma’aikatun tarayya suke gujewa yin bayanin yadda kuka batar da kudin da aka ware maku na yin ayyuka."

- Sanata Mathew Uroghide

Bola Tinubu ya soki APC

Asiwaju Bola Tinubu ya nuna tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsala a halin yanzu, ya zargi Gwamnatin Muhammadu Buhari a kan saukar darajar Naira.

Kwanan nan ‘dan takaran kujerar shugaban kasar ya yi ta kokorin wanke kan shi daga zargin sukar gwamnatin APC, sai ga shi ya sake wata baram-baramar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Matashiya Yar Arewa Da Dirarriyar Sura Ya Girgiza Intanet, Mijinta Ya Mata Yayyafin Kudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel