Bankuna Sun Bamu Kunya Kan Sabbin Takardun Kudi, Gwamnan CBN

Bankuna Sun Bamu Kunya Kan Sabbin Takardun Kudi, Gwamnan CBN

  • Gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankunan kasuwanci sun basu kunya
  • Gwamnan ya amsa gayyatar da kwamitin wucin gadi na majalisar wakilan tarayya ya aike masa a yau Talata
  • Da yake jawabi a gaban yan majalisun, Emefiele yace tsarin sauya takardun kuɗin naira ya haifar da sakamako mai kyau

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce bai ji daɗin yadda abubuwa suka tafi ba a wannan sabon tsarin, inda ya ce sun gano ana amfani da sabbin kudi a wurin shagalin sharholiya.

Gwamna ya ce hakan ya nuna bankunan kasuwanci sun take umarni da ƙa'idojin da CBN ya basu game da sabbin takardun N200, N500 da N1000 da aka canja.

Gwamnan CBN a Majalisa.
Bankuna Sun Bamu Kunya Kan Sabbin Takardun Kudi, Gwamnan CBN Hoto: @aminiya
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Emefiele ya yi wannan jawabin ne yayin da yake ƙarin haske kan sabon tsarin canja kuɗi a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ɗan Takarar Gwamna a 2023 Kazamin Hari, Sun Bude Masa Wuta

Yace bisa tilas babban bankinn ƙasa ya jawo Jami'an tsaro da hukumomin yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi cikin lamarin domin damƙe masu zagon ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene amfanin sauya kuɗin ga tattalin arziki?

Gwamnan CBN ya ƙara da bayanin cewa sabon tsarin ya fara haifar da ɗa mai ido sakamakon har yanzun hauhawar farashi bai ɗaga ba kuma tattalin arziki bai ƙara lalacewa ba.

Godwin Emefiele ya bayyana cewa garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da wasu muggan laifuka sun ragu sanadin tsarin canja kuɗin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A bayanansa, ya ce aikata manyan laifukan sun ragu ne saboda masu hannu a lamarin suna tsoron yawo da kuɗin haram wanda suka karɓa daga iyalan waɗanda suka yi garkuwa da su.

Muna da Isassun Sabbin Takardun Kudi a Wurinmu, CBN Ya Jaddada

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ta Fara Sabon Tsarin da Mutane Zasu Ji Dadi Wajen Samun Sabbin Kuɗi

A wani labarin kuma Babban bankin Najeriya ya jaddada cewa akwai isassun sabbin takardun kuɗi domin amfanin yan Najeriya

Jami'ar babban bankin, Lydia Alfa, ce ta faɗi haka yayin da ta fita yawon sanya ido kan yadda sabon tsarin ke tafiya a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Ta kuma shawarci 'yan Najeriya kar su yi jinkiri ganin cewa akwai sauran lokaci kafin 10 ga watan Fabrairu su yi duk me yuwuwa su tabbatar sun ba da tsoho an musanya masu da sabon kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel