Buhari Ya Jawo Wanda Obasanjo, 'Yaradua Suka Dauko a Jiki, Ya Damka Masa Mukami

Buhari Ya Jawo Wanda Obasanjo, 'Yaradua Suka Dauko a Jiki, Ya Damka Masa Mukami

  • Muhammadu Buhari ya zabi Olusegun Awolowo a matsayin Sakataren da zai kula da kwamitin AfCFTA
  • Mista Olusegun Awolowo ya yi aiki da gwamnatocin Obasanjo, Yar’adua da na Dr. Jonathan a Najeriya
  • Sabon Sakataren ya yi shekaru kusan 10 yana rike da NEPC, sannan ya taba yin aiki a ma’aikatar FCTA

Abuja - Muhammadu Buhari ya amince da nadin Olusegun Awolowo a matsayin Sakataren AfCFTA da ke aiki a kan sha’anin kasuwanci a Afrika.

Rahoton da The Guardian ta fitar a ranar Talata, 31 ga watan Junairu 2023 ya ce Olusegun Awolowo zai yi shekaru hudu yana rike da mukamin.

Wa’adin Awolowo ya fara a ranar 19 ga watan Disamban 2022, zai rabu da kujerar a shekarar 2026.

AfCFTA shi ne babban kwamitin da yake aiki domin ganin an wanzar da kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afrika ba tare da wani takunkumi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Rikirkice, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar Kwana 25 Gabanin Zaben 2023

Aiki AfCFTA a Afrika

A matsayinsa na Sakatare, Mista Awolowo zai fito da yadda AfCFTA zai yi aiki, sannan kuma ya hada-kai da duka sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton Premium Times ya ce aikin Awolowo ne ya duba yadda Najeriya za ta ci moriyar tsarin da aka fito da shi domin bunkasa tattalin kasashen Afrika.

Buhari
Shugaba Buhari a jirgi Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Sanarwar Femi Adesina

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bada sanarwar nadin mukamin da aka yi wa masanin shari’ar da ya yi karatu a Ogun.

Sakataren AfCFTA ya yi digirinsa a fannin shari’a ne a jami’ar ta jihar Ogun wanda yanzu aka canza mata suna zuwa jami’ar Olabisi Onabanjo a jihar.

Sanarwar Femi Adesina ta ce Awolowo ya yi aiki da gwamnatin Olusegun Obasanjo da kuma Marigayi Umaru Musa Yar’Adua a lokacin su na mulki.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Aiki a FCTA da NEPC

Tsakanin shekarar 2007 har zuwa 2011, Awolowo ne Sakataren harkar cigaban al’umma da sha’anin sufuri a karkashin ma’aikatar FCTA a Abuja.

A wani rahoton, an ji sabon sakataren ya shugabanci hukumar NEPC mai kula da harkokin fita da kaya zuwa ketare tun daga shekarar 2013 har 2022.

Bakar siyasa a Ribas

Idan za a koma siyasa, za a ji labari cewa ‘Dan Gwamnan jihar Ribas a Jam’iyyar APC ya ce wasu miyagu sun je filin taro, sun dauke masu Darektan zabe.

A baya haka ya faru da ‘Yan takaran Jam’iyyun adawa; Dumo Lulu-Briggs da Magnus Abe, saboda haka aka bukaci a kori kwamishinan ‘yan sandan Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel