Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Yar Arewa Da Dirarren Jiki Ya Dauka Hankali, Mijinta Ya Mata Liki a Taro

Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Yar Arewa Da Dirarren Jiki Ya Dauka Hankali, Mijinta Ya Mata Liki a Taro

  • Wata matashiya yar arewa mai ji da kyawun fuska da dirarren jiki ta yi fice a manhajar TikTok
  • Wani bidiyo da ya yadu a dandalin ya nuno kyakkyawar matar tana jawabi a taron jama’a masu yawan gaske
  • Yayin da take magana da dirarren jikinta a bayyane, mijinta ya fito cike da Alfa bari sannan ya fara lika mata bandir-bandir din kudi

Wani hadadden bidiyo da aka yada a soshiyal midiya ya nuno wani magidanci mai tsananin alfahari yana nuna kaunarsa ga kyakkyawar matarsa.

A wani bidiyo mai kayatar da zuciyar mai kallo, an gano dirarriyar matar tsaye a gaban jama’a tana koro jawabi kuma nan take mijin nata ya ji ta burge shi.

Kyakkyawar maya da mijinta
Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Yar Arewa Da Dirarren Jiki Ya Dauka Hankali, Mijinta Ya Mata Liki a Taro Hoto: @northern_hypelady/TikTok
Asali: UGC

Bidiyon ya hasko mijin yana tunkaro kan mumbarin taron sannan ya yi wa matar tasa yayyafin kudi bandir-bandir inda ita kuma ta dunga murmusawa.

Kara karanta wannan

Wasu Sun Kona Gidan ‘Dan Takaran APC, Mutane Sun Cafke Wanda Ya Yi 'Aika-Aikar'

Jama’a sun gaggauta gano kyawun matar mai tsuma rai da kuma dirarriyar surar da take dauke da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a sun yi martani

@damien65 ya ce:

“Idan Ina da irin wannan a gida. Ba zan taba cin amanar matata ba.”

@khadee100 ta ce:

“Ta zo ta baje masa kayansa a bainar jama’a. Wasu mazabar basu da kishi gsky.”

@199abu ya ce:

“A ina suke samun irin wannan matan Ina bukatar daya cikin gaggawa.”

@laughinpio ta ce:

“Ba na jin turanci kuma ban san yadda ake turanci ba amma menene amfanin wannan kudaden dukka.”

@huawabello ta ce:

“Wannan yar arewar ta cika tsaf faaaaa.”

@beffjezos25 ya ce:

“A matsayina na inyamuri, zan iya auren Bahaushiya? Kawai Ina son yanayin yan arewa ne kuma wadannan mata sun hadu.”

Kalli bidiyon a kasa

Bidiyon yadda wasu matasa suka yi ruwan bandir-bandir din sabbin kudi a wajen biki ya ta da kura

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wasu matasa suna lika sabbin kudaden da CBN ya sauya a wajen wani biki.

Babban abun da ya tunzura yan Najeriya da dama shine ganin mutane na wahala don ganin sun samu kudin koda kadan ne amma babu su a gari sai ga shi wasu sun samu fiye da kima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel