Yan Bindiga Sun Harbe DPOn Yan Sanda Har Lahira a Jihar Benuwai

Yan Bindiga Sun Harbe DPOn Yan Sanda Har Lahira a Jihar Benuwai

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kashe DPO na rundunar yan sandan ƙasar nan a jihar Benuwai dake arewacin Najeriya
  • Ciyaman na karamar hukumar Gwer ta yamna yace DPO na kan hanyar zuwa ɗauko wasu yan sanda maharan suka bude masa wuta
  • Mai magana da yawun hukumar yan sandan Benuwai ta tabbatar da faruwar lamarin, tace a saurari karin bayani

Benue - Wasu 'yan bindiga sun kashe DPO na hukumar yan sanda a ƙaramar hukumar Gwer ta yamma, jihar Benuwai dake arewa ta tsakiya a Najeriya.

Wani ganau ya ce DPO ya rasa rayuwarsa ne yayin da 'yan ta'addan suka mamayi Titin Naka-Makurdi wanda duk ya lalace da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Hukumar yan sanda.
Yan Bindiga Sun Harbe DPOn Yan Sanda Har Lahira a Jihar Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Shugaban ƙaramar hukumar Gwer ta yamna, Andrew Ayande, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Daily Trust ta wayar salula.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ɗan Takarar Gwamna a 2023 Kazamin Hari, Sun Bude Masa Wuta

Ya bayyana cewa Marigayi DPO, wanda ke jagorantar Caji Ofis din Naka, ya taho a Mota shi kaɗai zai je ɗauko jami'an yan sanda da aka tura aiki kan Titin, ba zato 'yan bindigan suka bude masa wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ciyaman din ya kara da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan ko maharan sun haɗa da wasu motocin da suka bi Titin a wannan lokaci, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shugaban ƙaramar hukumar yace bayan DPO an kashe wani mai suna Terhemba Tion da safiyar ranar Talata yayin da yan ta'adda suka farmaki ƙauyensu a Gwer ta yamma.

Yace mamacin ya rasa rayuwarsa ne a ƙauyensu Mbadyugh Tse -uhon dake yankin gundumar Sengev, ƙaramar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benuwai.

Wane mataki rundunar yan sanda ta ɗauka?

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan Benuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da kashe DPO wanda ta bayyana sunansa da, SP. Mamud Abubakar.

Kara karanta wannan

"Ba Zaman Lafiya" Gwamna Wike Ya Sake Fusata, Ya Maida Zazzafan Martani Kan Abu 1 a PDP

Anene ta ce, "Tabbas DPO na Naka ya rasa ransa, cikakken bayani kan lamarin zai biyo baya nan ba da jimawa ba."

A wani labarin kuma An Kama Daya Daga Cikin Miyagun Da Suka Yi Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa A Najeriya

Gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa gamayyar jami'an tsaro sun kama mutum daya da ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a jihar.

A cewar gwwamnan, wanda ake zargin yabfara bayani kuma yana taimaka wa jami'ai domin ceto mutanen da yan ta'addan suka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel