Atiku Ya Mayar da Martani Yayin da Tinubu Ya Kira Shi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

Atiku Ya Mayar da Martani Yayin da Tinubu Ya Kira Shi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

  • A wannan karon ma Bola Tinubu ya sake yin wata katobara yayin da yake magana a gaban masoyansa a Akwa Ibom
  • Tinubu ya saba kwafsawa a gaban jama’a tun bayan da ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe nan kusa
  • Abokin hamayyar Tinubu a PDP, Atiku Abubakar ya ce, yawan subut da bakan Tinubu ba abu bane da ya kamata a yi shuru a akai

FCT, AbujaDan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, yawaitar kwafsawar dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu babban abin kunya ne ga Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan nea cikin wata sanarwa ta bakin hadiminsa a harkar yada labarai, Phrank Shaibu a ranar Litinin 30 ga watan Janairun 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya koka da cewa, halin da Tinubu ya fara nunawa kamar wasa yanzu ya fara zama babban abin takaici ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Tinubu ya kwafsa, Atiku ya caccake shi
Atiku Ya Mayar da Martani Yayin da Tinubu Ya Kira Shi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A shafinsa na Twitter, Shaibu ya koka da yadda Tinubu ke kubutar baki, inda yace hakan matsala ne ga tsaron kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yiwa Tinubu kaca-kaca

Kadan daga abinda uake cewa:

“Daga fara neman takara, Tinubu ya yi subut da baka har sau 20 bainar jama’a. Wadannan subut da baka, da suka jawo ban dariya a kafar yanar gizo, yanzu sun wuce abin dariya sun koma abin takaici kuma abin kunya ga kasar da ke neman tsira.
“Matsalar kwakwalwarsa a bayyane take kuma ta nuna hadari ga tsaron kasa. Mutumin da bai da saitin kwakwalwa ba zai iya mulkin kasa ba.”

A fahimtar Atiku, tunda dai Tinubu babbar kujera yake nama a Najeriya, bai kamata a raina abin da yake fada ba.

Atiku ne tsohon shugaban majalisar dattawa a kwafsawar Tinubu

A tun farko, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu ya kalli masoyansa ya yi subut da baka wajen tabo kundin Atiku.

Kara karanta wannan

Ahaf: An kuma, Tunubu ya sake yin wata katobarar da tafi na baya game da Atiku

Ya ce, Atiku ne tsohon shugaban majalisar dattawa na Najeriya da siyar da kayayyaki da yawa na kasar nan a lokacin da yake aiki.

A kuma cewarsa, su suka daura Atiku a kujerar shugaban majalisa a shekarun da bai bayyana yaushe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel