Yadda na Tsere, Na Burma Aikin Soja Saboda Tsoron Ayi Mani Aure Inji Buhari

Yadda na Tsere, Na Burma Aikin Soja Saboda Tsoron Ayi Mani Aure Inji Buhari

  • Muhammadu Buhari ya ce gudun ayi masa auren wuri, shiyasa ya shiga aikin sojan kasa a Najeriya
  • Shugaban kasar ya dauko wannan tsohon tarihi ne a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Daura
  • Buhari ya godewa Allah a kan irin damar da ya samu, har aka samu shugaban kasa daga kauyensu

Daura - Muhammadu Buhari ya bude littafin tarihi, ya bada labarin abin da ya tursasa shi shiga aikin soja saboda an matsa masa da maganar aure.

Tribune ta rahoto Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 27 ga watan Junairu 2023, yana cewa kokarin aurar da shi ne ya jawo ya zama soja.

Buhari ya ziyarci fadar Sarkin Daura, Mai martaba Faruk Umar Faruk bayan kaddamar da tituna da Gwamnatin Aminu Bello Masari ta gina.

Shugaban Najeriyan ya bada labari yadda ya fara samun aiki a wani shago a Daura, amma dole ya tsere zuwa gidan soja da aka huro wuta ya yi aure.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bada Hutu Na Kwanaki A Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

"Game da shiga soja, na ba Gwamna Aminu Bello Masari labarin yadda na bar Daura, na shiga soja. Haka Allah ya tsara, ka na naka, Allah Ya yi na shi."

- Muhammadu Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari
Buhari a Sanagal Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari ya ga mutuwa tsirara

Punch ta rahoto tsohon sojan yana bada labarin irin kalubalen da ya gani a lokacin yakin basasa, ya ce a gabansa ake mutuwa, amma shi din ya yi rai.

Buhari yake cewa ya gamu da fadi-tashi dabam-dabam a rayuwa, sannan ya godewa Ubangiji a kan yadda ya rika ba shi kariya a tsawon shekarun nan.

Daura ta samu Shugaba a Najeriya

Mai girma Muhammadu Buhari ya ce Ubangiji ne ya ba shi damar da zai bautawa kasarsa, ya ce an san Najeriya da mabanbantan kabilu da addinai.

A cewar shugaban Najeriyan, a samu shugaban kasa daga garinsa na Daura, abin alfahari ne, ya kuma ce a nan zai zauna idan ya bar fadar Aso Villa.

Kara karanta wannan

Karshen mulki: Saura kwanaki Buhari ya sauka, ya tura sako mai daukar hankali ga 'yan Najeriya

Ayyukan da aka kaddamar a Katsina

A ziyarar da ya kawo, Buhari ya bude wani babban asibiti da makarantar sakandare da Gwamnan jihar Katsina ya gina a karamar hukumar Musawa.

Baya ga haka, jaridar ta ce an kaddamar da titunan Gora-Makauraci-Malamawa, Sandamu-Baure-Babban Mutum da na Gurjiya -Sandamu-Karkarku.

'Yan siyasa ke jawo rikici - Abdulrahman Dambazau

Rahoton da muka fitar, ya bayyana cewa a ranar Alhamis dinnan, Kungiyar nan ta I Am Change ta shirya taro inda aka tattauna batun tsaro a Abuja.

Janar Abdulrahman Dambazau ya samu gabatar da jawabi wajen zaman, tsohon hafsun sojin ya zargi 'yan siyasa da kawo rigingimu da rabuwar kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel