Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bada Hutu Na Kwanaki A Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bada Hutu Na Kwanaki A Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke shirin barin ofis cikin yan watanni daga yanzu yana da wasu ayyuka da zai yi a wasu jihohi cikin yan kwanakin nan masu zuwa
  • Daya cikin cikin jihohin ita ce Katsina, shugaban kasar zai ziyarci babban jihar ta arewa domin ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnati ta yi
  • Saboda ziyarar shugaban kasar da ake shiryawa, gwamnan jihar Katsina ya bada hutun kwanaki biyu saboda ma'aikatansa su yi shirin tarbar Buhari

Katsina - Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya bada hutun kwanaki biyu ga daukakin ma'aikatan gwamnati a jihar.

PM News ta rahoto cewa Masari ya ayyana Alhamis 26 ga watan Janairu da Juma'a 27 ga watan Janairu a matsayin ranakun hutu ga ma'aikatansa domin su samu damar fitowa su tarbi Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Katsina: Buhari ya Isa Jihar Katsina Daga Dawowarsa Senegal, Gwamna Masari da Ayarinsa Sun Masa Tarbar Karamci

Buhari a Katsina
Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bada Hutu Na Kwanaki A Jiharsa, Ya Bayyana Dalili. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari ya isa jihar Katsina a daren ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, daga Dakar, Senegal bayan ya halarci taron kasa da kasa kan aikin noma.

Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar Katsina

Sakataren dindindin na ma'aikatar al'adu da harkokin cikin gida na jihar, Alhaji Sani Kabomo ya ce Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Gwamna Aminu Masari ya yi, Sahara Reporters ta rahoto.

Ya ce hutun kwana biyun da aka bada ba zai shafi ma'aikatan hukumomin gwamnatin tarayya ba, ma'aikatan banki da sauran masu ayyuka da ake bukatarsu a koda yaushe.

Gwamnan Jihar Katsina zai kashe Naira miliyan 500 don shirin tarbar Shugaba Buhari a jiharsa

Tunda farko kun ji cewa Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yarda a ayi amfani da kudi naira miliyan 500 domin tara al'umma da za su tarbi Shugaba Muhammadu Buhari yayin ziyarar da zai kawo a jihar.

Kara karanta wannan

Ma'aikata Da Jama'ar Gari Sun Rabauta da Hutun kwana Biyu A Jihar Katsina Dan Zuwan Buhari

Jaridar Leadership ta rahoto cewa gwamnan zai samo kudaden ne daga asusun kananan hukumomi da ke jihar.

Wata wasikar amincewar kashe kudi mai dauke da kwanan wata na 18 ga watan Janairu wacce ta bayyana a kafafen sada zumunta ta ce za a fitar da kudi har N14,695,588.00 ne daga kowanne karamar hukuma cikin 34 da ake da su a Jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel