Tinubu Ya Aikawa Sarakunan Kano 2 Sako a Kan Babban Rashin da Aka Yi Masu

Tinubu Ya Aikawa Sarakunan Kano 2 Sako a Kan Babban Rashin da Aka Yi Masu

  • Bola Ahmed Tinubu ya taya gidan Sarki Abdullahi Bayero jimamin rasuwar Hajiya Fulani Hasiya Bayero
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya aika da ta’aziyyarsa zuwa ga Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero
  • Jawabin Bola Tinubu ya ce duk wanda ya san Marigayiya Fulani Hasiya Bayero, ba zai manta ta ba

Kano - Bola Ahmed Tinubu ya aika da ta’aziyya ga Sarakunan Kano da Bichi watau Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero a dalilin rashi da aka yi.

The Nation ta ce ‘dan takaran kujerar shugaban kasar na jam’iyyar APC a zaben 2023, ya aika sakon ta’aziyyarsa na mutuwar Hajiya Fulani Hasiya Bayero.

Fulani Hasiya Bayero ta rasu a ranar Talata da ta gabata, 17 ga watan Junairu 2023. Marigayiyar ‘yar uwa ce ga tsohon Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fallasa Naja’atu, Ta Tona Ainihin Dalilin Komawarta Wajen Atiku

Jawabin ya fito ta bakin Mai taimakawa ‘dan takaran wajen yada labarai da sadarwa, Abdulaziz Abdulaziz.

An yi rashin Fulani Hasiya

Abdulaziz yake cewa Fulani Hasiya mutumiyar kirki ce mai kaunar jama’a, wanda tayi kokari wajen rike zumuncin da yake tsakanin gidajen sarauta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto Tinubu yana mai cewa ba gidan Bayero kadai aka yi wa rashin ba, ya ce duk wanda ya taba haduwa da Marigayiyar zai ji mutuwar.

Sarakuna
Sarakunan Kano da Bichi Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

"Za a tuna da ita musamman wajen murmushin da take yi mai shiga rai da kirki da take yi wa kowa."

- Bola Tibubu

Jawabin ta’aziyyar ya ce Fulani Hasiya ta bar ‘ya ‘ya shida a Duniya da kuma jikoki da-dama. Daga cikin jikokin da ta bari akwai Dr. Maryam Shettima.

Dr. Maryam Shettima ta na cikin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima, ta na aiki da sashen dabaru, tsare-tsare da na jawo jama’a.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

Jaridar ta ce ‘dan takaran na APC ya roki Ubangiji ya Aljannat-al-Firdaus ce makomarta, ya kuma ba gidan sarautar Bayero hakurin jure wannan rashi.

Kiran Jabir Sani Maihula

Rahoto ya zo cewa Malamin hadisin Annabi SAW, Jabir Sani Maihula ya yi kira ga hukuma a kan canjin manyan takardun N1000, N500 da N200 da aka yi.

Dr. Jabir Sani Maihula yake cewa an dade bankuna su na raba tsofaffin kudi ga mutane, saboda haka ya roki hukumomin kasar da su sake duba wa’adin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel