Shugaba Buhari Ya Dauki Matakin Karshe da Zai Sa a Daina Ganin Dogayen Layin Fetur

Shugaba Buhari Ya Dauki Matakin Karshe da Zai Sa a Daina Ganin Dogayen Layin Fetur

  • Muhammadu Buhari ya yarda a kafa wani kwamiti da zai duba matsalolin wahalar man fetur
  • Shugaban kasar ne zai shugabanci kwamitin tare da karamin Ministansa na fetur, Mr. Timipre Sylva
  • Kwamitin zai tabbatar NNPC ya samar da isasshen man fetur, kuma ana saidawa a farashin gwamnati

Abuja - A ranar Talatar nan, Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mutum 14 da zai tabbatar an daina fama da wahalar fetur a Najeriya.

Daily Trust ta ce kwamitin zai dage wajen ganin an kuma saida fetur a kan farashin gwamnati. Hakan yana zuwa ne a lokacin da ake wahalar samun mai.

Mai girma Muhammadu Buhari zai jagoranci kwamitin tare da karamin Ministansa na harkokin man fetur, Cif Timipre Sylva a matsayin wani shugaban.

Rahoto ya ce sauran ‘yan kwamitin sun hada da Ministar tattalin arziki, tsare-tsare da kasafin kudi, da Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkar fetur.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

EFCC, DSS, NSCDC su na cikin kwamitin

A kwamitin akwai babban mai ba shugaban kasa shawara a harkar tattalin arziki, Shugaban hukumar DSS, shugabannin hukumomin kwastam da EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan akwai shugaban hukumar NSCDC tare shugaban ma’aikatar NMDPRA da takwaransa na NNPC, da gwamnan babban bankin Najeriya na CBN.

Shugaba Buhari
Muhammadu Buhari a Legas Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Akwai masu ba Ministan harkar fetur biyu a cikin kwamitin, daga cikinsu ne aka samu Sakatare.

Aikin da kwamitin zai yi - Horatius Egua

The Guardian ta ce kamar yadda Horatius Egua ya fitar da jawabi, shugaban kasa ya umarci NMDPRA ta tabbatar ana saida mai a tashohi a farashin gwamnati.

Egua shi ne mai ba karamin Ministan harkar fetur shawara wajen yada labarai da sadarwa.

Kwamitin zai yi aiki wajen duba yiwuwar gyaran matatun NNPC tare da bibiyar man da ake rabawa kullum domin sa ido a kan masu fita da shi zuwa ketare.

Kara karanta wannan

Gwamna Masari Ya Fitar da N500m don tara jama'a su tarbi Shugaba Buhari Ranar Alhamis

Buhari ya bada umarni ga NMDPRA cewa ta tabbata NNPC ta na shigo da man da ake bukata, sannan za ayi kokarin hana farashin dizil, kananzir da gas tashi.

An kai wa Peter Obi hari

Rahotanni sun tabbaar da cewa wasu miyagu sun aukawa Peter Obi da mutanensa a kan hanyarsu ta zuwa filin tashi da saukar jirgin sama a garin Katsina

Bayan nan, wasu ‘yan iskan-gari sun sake rutsa tawagar ‘Dan takaran jam’iyyar LP da ruwan duwatsu kamar yadda kwamitin neman takarar Obi ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel