Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon IGP a Matsayin Shugaban Hukumar PSC

Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon IGP a Matsayin Shugaban Hukumar PSC

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Solomon Arase a matsayin shugaban PSC
  • Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar shugaban kasa a zaman Sanatocin na yau Talata, 24 ga watan Janairu, 2023
  • Arase, tsohon Sufeta janar na rundunar yan sanda, zai gaji Musiliu Smith idan har majalisar ta amince da bukatar Buhari

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa Solomon Arase, tsohon Sufetan 'yan sanda na ƙasa (IGP) a matsayin shugaban hukumar jin daɗin 'yan sanda (PSC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa naɗin na gaban majalisar dattawa a halin yanzun domin tantancewa da amincewa.

Solomon Arase.
Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon IGP a Matsayin Shugaban Hukumar PSC Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar da Buhari ya aike masu wanda ta dogara da sashi na 153 (1) da kuma sashi na 154 (1) na kundin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa idan majalisar ta tabbatar da naɗin, Arase zai gaji Musiliu Smith, wanda shi ma tsohon Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Smith ya yi murabus daga kujerar shugaban hukumar PSC a shekarar da ta gabata a wani yanayi mai matukar ruɗani, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Bayan faruwar haka ne Clara Ogunbiyi, Alkali mai ritaya, ya karɓi ofishin a matsayin muƙaɗdashin shugaban hukumar.

Wanene Solomon Arase?

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jomathan ne ya naɗa Arase a matsayin Sufetan yan sanda na ƙasa IGP a shekarar 2015 bayan ya sallami Suleiman Abba bisa zargin rashin ɗa'a.

Kafin ya zama IGP, Mista Arase ya jagorancin sashin tattara bayanan sirri na rundunar 'yan sanda, sashin tara bayan aikata manyan laifuka da sashin bincike.

An haifi Arase a ranar 21 ga watan Yuni, 1956 a Ƙaramar hukumar Owan ta yamma, jihar Edo. Ya halarci jami'ar Ahmadu Bello Zariya (ABU) inda ya karanci kimiyyar siyasa ya kammala a 1980.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shugaban Majalisar Dattawa Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

Ya shiga aikin yan sanda shekara ɗaya bayan gama karatu ranar 1 ga watan Disamba, 1981. Ya sake komawa karatu ya yi digiri a fannin shari'a jami'ar Benin, ya yi digiri na biyu a jami'ar Legas.

Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai

A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa ya amince da naɗin Abdul Mutallab Muktar a matsayin Daraktan kamfanin FHFL a Najeriya

Shugaban kasa Buhari ya amince da wannan sabon nadin ne ta ofishin Ministar tattalin arziki da kasafin kudi, Zainab Ahmed.

Kafin ya samu wannan mukami, Mista Abdul Mutallab Muktar yana cikin manyan hadiman shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262