Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai, Ya Nada Sabon Shugaban FHFL

Shugaba Buhari Ya Cigaba da Yin Rabon Mukamai, Ya Nada Sabon Shugaban FHFL

  • Abdul Mutallab Muktar zai rike kujerar Babban Darekta kuma shugaban kamfanin FHFL a Najeriya
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin ta ofishin Ministar tattalin arziki da kasafin kudi
  • Kafin samun CEO a FHFL, tsohon ma’aikacin bankin yana aiki tare da Farfesa Ibrahim Gambari a Aso Villa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da Abdul Mutallab Muktar ya zama Babban Darekta kuma shugaban kamfanin nan na FHFL na kasa.

Kafin ya samu wannan mukami, The Nation ta ce Mista Abdul Mutallab Muktar yana cikin manyan hadiman shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Abdul Mutallab Muktar da wasu kwararru sun yi aiki wajen ganin gwamnatin nan ta cin ma manufofin gina abubuwan more rayuwa da noma abinci.

Wannan sabon nadi da aka yi ya fito ne daga bakin ma’aikatar tattali, kasafi da tsare-tsaren kudi na tarayya a yammacin Talata, 10 ga watan Junairu 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Dauki Sabbin Alkawurra a Bangaren Ilimi, Ya Bude Shafin Tallafin Kamfen 2023

Wanene Abdul Mutallab Muktar?

Sanarwar ta ce an haifi sabon shugaban na FHFL ne a ranar 9 ga watan Yunin 1975 a garin Katsina, ya shafe sama da shekaru 22 yana mu’amala da kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muktar ya yi muhimman aiki a baya, inda ya jagoranci ofisoshi da kamfanoni wajen ganin sun bunkasa kudin shiga tare da inganta kyawun aikinsu.

Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Babban Darektan kwararre ne a harkar banki, bunkasa kasuwanci, tsarin fansho da aikin gwamnati. Sai dai Legit.ng ba ta san tsawon wa'adin aikinsa ba.

Karatun da Muktar ya yi a gida da waje

Jaridar Daily Trust ta ce Muktar mai shekara 47 a Duniya ya samu digirinsa na farko da digirgir na MBA a ilmin sanin kasuwanci daga jami’ar ABU a Zariya.

Tsohon mai ba shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa shawara ya yi digirgir a kan kula da kasuwancin kasashen waje a wata jami’ar Berlin a Jamus.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Yi Sabuwar Nadi Mai Muhimmanci Gabanin Babban Zaben 2023

Har ila yau, Muktar ya rike babban jami’in kula da alaka da cigaban kasuwanci a Access Bank da wasu mukamai a Anchor Pension Managers Ltd da FBN.

An kafa Family Homes Funds Limited (FHFL) ne domin ganin mutane sun mallaki gidaje.

Komai lafiya a APC?

Ku na da labari Bola Tinubu ya doke Rotimi Amaechi, Yemi Osinbajo da Ahmad Lawan da wasunsu a wajen samun takarar shugabancin Najeriya a APC.

Ana tunanin Irinsu Rochas Okorocha, Ogbonnaya Onu, Tunde Bakare da Nwajiuba Chukwuemeka sun fita daga harkar yi wa APC kamfe a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel