'Yan ISWAP Sun Hadu da Ajalinsu a Harin Kwantan Bauna da Suka Kaiwa Sojin Najeriya a Borno

'Yan ISWAP Sun Hadu da Ajalinsu a Harin Kwantan Bauna da Suka Kaiwa Sojin Najeriya a Borno

  • Dakarun sojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai da ke Borno sun ragargaza mayakan ISWAP da suka kai musu harin kwantan bauna
  • An gano cewa, mayakan ta'addancin sun bayyana a motocin yaki, MRAP da babura inda suka farmaki mayakan a Damboa da ke jihar Borno
  • Gamayyar dakarun sojin kasa da na sama na Najeriya ne suka yi ruwan wuta kan mayakan inda suka halaka da yawa daga ciki tare da raunata wasu

Borno - Mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP masu tarin yawa a ranar Litinin sun hadu da ajalinsa a hannun dakarun birged na 25 na rundunar Operation Hadin Kai da ke Damboa a jihar Borno.

Taswirar Borno
'Yan ISWAP Sun Hadu da Ajalinsu a Harin Kwantan Bauna da Suka Kaiwa Sojin Najeriya a Borno. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

An tattaro cewa, 'yan ta'addan sun hadu da gagarumar rashin nasara yayin da suka kaddamar da harin kwantan bauna a tawaga a kauyen Komala da ke kan titin Damboa zuwa Maiduguri.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3

Wata majiyar tsaro ta sanar da Zagazola Makama, kwararriyar wallafa kan lamarin tsaro da kiyasi a yankin tafkin Chadi, cewa 'yan ta'addan da suka bayyana amotocin Hilux, MRAP da babura, sun kai farmaki kan dakarun da ke sintiri.

Majiyar tace dakarun sun yi hanzari yin martani da ruwan wuta mai zafi ga 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace kokarin da taimakon dakarun sojin sama da na kasan ne ya kai ga halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa yayin da wasu suka arce.

"Mun yi nasarar kwace motar yaki daya, MRAp tare da babura uku daga 'yan ta'addan.
"'Yan ta'addan ISWAP na cigaba da fuskantar matsanancin rashin nasara a hannun dakarun soji. A ranar 13 ga watan Janairu, dakarun sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa tare da lalata MRAP yayin da suka farmaki sojoji a Azir.

Kara karanta wannan

An Kama Sarakuna Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya

"Sakarkarun sun yi yunkurin gwada sa'arsu a kan mu amma Allah na bayanmu. Nasara tana hararo mu."

- Yace.

Hankalin fasinjojin jirgin kasa ya tashi bayan sun makale a dajin Kogi

A wani labari na daban, fasinjoji sun shiga tashin hankali mai tarin yawa bayan jirgin kasan ya lalace musu a cikin dajin Kogi yayin da suke hanyarsu ta Itakpe daga Warri.

Tuni hukumar kula da sufurin jiragen kasa suka hanzarta kai motoci tare da kwashe fasinjojin domin gudun 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel