Dubu Ta Cika: An Kama Daya Daga Cikin Maharan Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

Dubu Ta Cika: An Kama Daya Daga Cikin Maharan Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

  • Jami'an tsaro 'Yan banga a garin Zuba dake yankin birnin tarayya Abuja sun cafke wani da ake zargi da hannu a kai harin jirgin kasa
  • Bayanai sun nuna cewa yan bangan Miyetti Allah ne suka taimaka aka kama mutumin mai suna Bello Yellow ranar Lahadi
  • Yan banga sun fara bincikarsa kafin su miƙa wa yan sanda kuma sun gano wasu abubuwa a tattare da shi

Abuja - 'Yan banga a garin Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja sun damƙe wani, Bello Yellow, da ake zargin yana da alaƙa da harin jirgin kasan Kaduna-Abuja.

Jaridar Daily Trust tace wanda ake zargin ya shiga hannu ne da safiyar ranar Lahadi yayin da wata Mota ta sauke shi a kusa da Tashar motocin Dan-Kogi.

An kama wani da ake zargi a Abuja.
Dubu Ta Cika: An Kama Daya Daga Cikin Maharan Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wani ɗan Banga ya bayyana cewa jami'ansu na cikin Miyetti Allah watau 'Yan bangan Miyetti Allah ne suka fara ganin Yellow.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Nan take suka ankarar da 'Yan Bangan da ke aiki a Tashar motocin domin su kawo masu agaji. Aka cafke shi sannan suka tasa keyarsa zuwa Ofishin mu."
"Anan aka tsare shi kuma aka fara bincike a kansa kafin daga bisani muka miƙa wa rundunar 'yan sanda da misalin ƙarfe 4:00 na Subahi."

Abinda aka gano bayan binciken farko

Jami'in dakarun 'Yan Bangan ya ce yayin binciken wanda ake zargi, sun sami tsabar kudi N103,000 da kuma Sigari guda uku da Letar kunna wuta.

Ya kara da cewa DPO na Caji Ofis din Zuba da kansa ya je Ofishin Yan Banga tare da jami'ansa suka ɗauki wanda ake zargin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

A cewarsa, "Duk da Yan bangan Fulani sun gaya mana sunansa Bello Yellow, shi kuma ya faɗa masa sunansa Bature Shabe kuma ya taso daga Ilorin, jihar Kwara za shi dajin Shenagu dake kusa da Zuba wurin yayansa, Alhaji Shabe."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Yi Babbar Ɓarna a Jiha

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Yi Babbar Ɓarna a Jihar Enugu

Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin yan bindigan sun yi awon gaba da mutane shida cikinsu har da matashi ɗan bautar ƙasa.

Wani shugaban al'umma da ya tabbatar da kai harin ya ce da kyar suka sha bayan maharan sun bude wa motarsu wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel