An Kama Wani Makaho da Kuturu Dauke da Tarin Ganyen Wiwi a Jihohin Osun da Kano
- Hukumar NDLEA a Najeriya ta yi nasarar kame wasu mutane biyu da aka zargin su da aikata harkallar tabar miyagun kwayoyi
- An kama wani makaho da ke ajiyar tabar wiwi a jihar Osun, an bayyana irin kudaden da ake ba shi na ajiyar kayayyakin
- Hakazalika, a jihar Kano, an kama wani kuturu da ke harkallar miyagun kwayoyi, tuni aka kwato kayayyaki a hannunsa
FCT, Abuja - Jami’an hukumar NDLEA sun yi nasarar kame wani makaho mai shekaru 67, Aliyu Adebiyi, wanda aka samu kiligiram 234 na tabarar wiwi a gidansa.
An ce jami’an sun gano wannan tarin haramtaccen kaya ne a gidan makahon da ke kauyen Sokoto a yankin Owena Ijesa a karamar hukumar Atakumosa ta gabas a jihar Osun.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana wannan batu a ranar Lahadi a Abuja, inda ya bayyana nasarorin da hukumar ta samu, Daily Trust ta ruwaito.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/1a6297eebaa77482.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu
![Kuturu da makaho sun shiga hannu Kuturu da makaho sun shiga hannu](https://cdn.legit.ng/images/1120/9eef7abc0ddacce2.jpeg?v=1)
Asali: UGC
A cewar kakakin, makahon na yin ajiyar wadannan kayayyakin ne a kan kudi N6000 a duk wata, kuma tuni aka biya shi na watanni uku kafin zuwansu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An kama kutura dan harkalla a Kano
A wani yanayi irin wannan, jami’an sun kame wani kuturu, Haruna Abdullahi mai shekaru 45 a garin Garko ta jihar Kano a ranar Alhamis 19 ga watan Janairu.
An kama Haruna ne dauke da wasu haramtattun kayayyaki da suka hada da tabar wiwi, tarin kwayoyin aji-garau, masu sa bacci na ‘Diazepam’ da ‘Exol’.
Hakazalika, Babafemi ya ce hukumar ta kuma yi nasarar dakile yunkurin shigo da kilogiram 126.95 na hodar iblis da aka boye a ganyen shayi.
A cewarsa, an kama kayan ne filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke jihar Enugu da kuma bakin ruwan Tin Can da ke Legas, rahoton The Nation.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/688acae7b82d76b4.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC
Ya kara da cewa, ana zargin an shigo da kayayyakin ne daga kasashen waje; Brazil da Kanada don yin harkallarsu a Najeriya.
An kama tsoho mai safarar makamai
A wani labarin kuma, kun ji yadda jami'an tsaro a Najeriya suka yi nasarar kame wani tsoho da wasu mutu, biyu bisa zarginsu da harkallar makamai.
Rahoto ya ce an kama tsohon mai shekaru 70; Sani Mani da wasu mutum biyu; Haruna Yahaya da Isa Haruna.
A cewar jami'an tsaro:
"Bincike ya nuna cewa Yahaya mamba ne na wani babban kungiyar masu aikata manyan laifuka da ke addabar mazauna yankin Tungan-Maje."
Asali: Legit.ng