‘Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekaru 70 da wasu 2 dauke da makamai
- Rundunar 'yan sandan birnin tarayya ta ce ta cafke wasu mutane uku a karamar hukumar Kuje dauke da makamai
- Daga cikin wadanda aka kama akwai dattijo mai shekaru 70, Sani Mani; Haruna Yahaya da Isah Haruna
- Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya, CP Sunday Babaji, ya ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
'Yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, sun cafke wasu mutane uku a karamar hukumar Kuje sakamakon samun su da makamai.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, mutanen da aka damke sun hada da wani dattijo mai shekaru 70, Sani Mani; Haruna Yahaya da Isah Haruna.
Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, CP Sunday Babaji, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi a hedikwatar rundunar, ya ce an kama wadanda ake zargin ne saboda hada kai wajen aikata manyan laifuka.
Har wayau, ana zarginsu da yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a yankunan Kuje da Tungan-Maje.
Ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin, Yahaya Haruna, a kasuwar Tungan-Maje yayin da yake dauke da makamin da aka kirkira a cikin gida.
"Bincike ya nuna cewa Yahaya mamba ne na wani babban kungiyar masu aikata manyan laifuka da ke addabar mazauna yankin Tungan-Maje," in ji shi.
Har ila yau, ya ce kamun Yahaya ne ya kai ga cafke sauran mutanen biyu da ake zargi, yana mai cewa za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya
A gefe guda, wasu mata biyu da yan sanda suka damke, sun bayyana yadda suke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashin daji, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Kakakin yan sanda na ƙasa, Frank Mba, a makon da ya gabata, ya bayyana wasu mutum 11 da jami'an suka damke, cikinsu harda mata guda biyu.
Ɗaya daga cikin matan, Aisha Ibrahim, yar shekara 30, ta zayyana yadda ta ɗauki bindiga AK-47 daga Lafia, jihar Nasarawa zuwa Kaduna.
Asali: Legit.ng