Sun Gama Da Ita: Bidiyon Baturiya Tana Yawo Babu Takalmi Kuma a Hargitse a Titin Lagas Ya Haddasa Cece-kuce

Sun Gama Da Ita: Bidiyon Baturiya Tana Yawo Babu Takalmi Kuma a Hargitse a Titin Lagas Ya Haddasa Cece-kuce

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata baturiya da ya bayyana inda aka gano ta cikin wani yanayi a hargitse a titin Lagas
  • An gano matar wacce ba a san ko wacece ba tana tafiya babu takalmi da wani dabbare-dabbaren ja a jikinta da kuma karan sigari a hannunta
  • Yayin da wasu suka alakanta halin da take ciki da shan miyagun kwayoi, wasu na ganin ko an yi asiri ne da ita

Wani bidiyon baturiya cikin mawuyacin yanayi babu takalmi a kafa ya bayyana a shafukan soshiyal midiya.

Wata matashiya da ta dauki bidiyon ta ce tana a hanyarta na zuwa siyan man fetur a Sangotedo, Ajah ne lokacin da ta hangi matar.

Baturiya
Sun Gama Da Ita: Bidiyon Baturiya Tana Yawo Babu Takalmi Kuma a Hargitse a Titin Lagas Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Ta yi zargin cewa an yi amfani da baturiyar ne wajen asiri inda ta bukaci mutane da su yi hankali, cewa babu wanda ya fi karfin ayi amfani da shi.

A bidiyon da aka wallafa a Instagram, an gano baturiyar da wasu dabbare-dabbare ja a fadin jikinta sannan hannunta na dama na dauke da karan sigari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun taru a wajen faruwar lamarin dauke da damuwa a fuskokinsu. An tattarop cewa an gano ta ne a ranar Juma'a, 20 ga watan Janairu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@big_hollywillz ya ce:

"Kun tabbata wannan shaidar alluran da ke jikinta ba miyagun kwayoyi bane da take antayawa kanta, don komai sai ku daura laifi kan gayu."

@blossoming_soul1 ya ce:

"Bata yi kama da wani ya yi asiri da ita ba. Idan kuma ya zamana ta zo neman sihiri ne sai abun ya koma kanta. Wadannan turawa da ke son sirkullen bakin fata."

@bigibk__ ta ce:

"Masu cewa an yi asiri da ita da sauransu.

"Wannan ya yi kama da aikin miyagun kwayoyi."

Uwa ta farma ango da naushi a wajen darin aure

A wani labari na daban, an kaure da rigima tsakanin wata amarya da angonta a hanyarsu ta zuwa wajen da za a daura masu aure.

Yayin da suke tafiya a tare da hannunsu cikin juna, sai amaryar ta dauke mijin nata da naushi lamarin da ya kai ga har sai da aka shiga tsakani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel