Abin da Ya Sa Mutane Za Su Koma Sayen Litar Fetur a Kan N800 Nan da Watanni 6

Abin da Ya Sa Mutane Za Su Koma Sayen Litar Fetur a Kan N800 Nan da Watanni 6

  • Wasu ‘yan kasuwa sun yi gargadi a kan gaggawan janye tallafin man fetur ba tare da an shirya ba
  • Wani shugaba na kungiyar IPMAN ya ce idan aka daina biyan tallafi, to litar mai za ta iya haura N800
  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hakikance a kan cire hannunta a kan abin da ya shafi kudin fetur

Abuja - Ganin yadda ake fama da wahala wajen samun man fetur a Najeriya, ‘yan kasuwa sun bayyana cewa farashin yana da daf da sake tashi.

A rahoton Punch na ranar Lahadi, 22 ga watan Junairu 2023, an samu labari cewa abin da ake sayen litar fetur a gidan mai zai yi matukar dagawa.

Manyan ‘yan kasuwa sun tsaida N800 a matsayin farashin lita da zarar Gwamnatin tarayya ta cire hannunta daga biyan tallafin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

An kusa zaben 2023, 'yan bindiga sun sheke wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a wata jiha

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta koka da cewa dole a cire kason da ake biya domin a hana farashin fetur tashi domin kudin ya yi yawa sosai.

Karin fiye da 400%

A wata hira da jaridar tayi da wasu daga cikin masu kasuwancin fetur a kasar nan, sun tofa albarkacin bakinsu a game da shirin janye tallafin a bana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan kasuwa su na ganin daga kusan N200 da jama’a suke sayen litar fetur a kan farashin gwamnati, janye tallafin zai jawo farashin ya nunku hudu.

Gidan mai
Gidan mai a shekarun baya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wannan ya sa ‘yan kasuwan suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da duk abubuwan da ake bukata na more rayuwa kafin a dauki matakin nan.

"Idan gwamnati ba ta dauki matakan da suka kamata ba, kuma su na so su cire tallafin fetur, lamarin zai yi muni fiye da haka.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta Sanar da Sabon Farashin Litar Fetur, An Amince da Karin 8.8% a Najeriya

Ta ya za ka janye tallafi kuma ba ka da kayan nan (fetur). Idan gwamnati ta cire tallafin, ina kayan?
Watakila idan aka cire tallafin fetur, yadda ake sayen dizel tsakanin N800-N900, haka za a koma sayen litar fetur, ko fiye da haka.

- Mohammed Shuaibu

Mohammed Shuaibu wanda shi ne Sakataren kungiyar IPMAN na reshen Abuja-Suleja ya ce akwai bukatar gwamnati ta fito ta fadawa al’umma gaskiya.

A cire Keyamo daga FEC - PDP

A gefe guda, ku na da labari cewa jam’iyyar PDP ta dage cewa sai an sauke Festus Keyamo daga kujerar Minista saboda cin amanar da aka damka masa.

A lokacin da kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar yake wannan kira ne kuma Mai girma Shugaban Najeriya yake taya Ministan murnar cika shekaru 53.

Asali: Legit.ng

Online view pixel