Gwamnati ta Sanar da Sabon Farashin Litar Fetur, An Amince da Karin 8.8% a Najeriya

Gwamnati ta Sanar da Sabon Farashin Litar Fetur, An Amince da Karin 8.8% a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da ‘yan kasuwa cewa su kara kusan 9% a kan abin da suke saida fetur a yau
  • An yi kari a manyan tashohi, saboda haka litar man fetur zai tashi a kusa duka gidajen man da ke kasar
  • Daga N170 da dillalai suke saida lita a kan sari, manyan ‘yan kasuwa sun koma sayen mai a kan N185

Abuja - Rahoto ya zo cewa Gwamnatin tarayya ta amince da karin 8.8% a kan farashin litar man fetur, yanzu kudin ya tashi daga N170 zuwa N185.

Vanguard da ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 20 ga watan Junairu 2023, ta ce mafi yawan gidajen mai su na saida fetur ne a farashin da ya zarce haka.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da wata sanarwa a karshen makon, ta umarci ‘yan kasuwa su koma yin aiki da sabon farashi da aka amince da shi.

Kara karanta wannan

NDLEA Tayi Abin da Ba a Taba Yi ba a Tsawon Shekara 33 a Karkashin Buba Marwa

Gidajen man da ke karkashin kungiyar ‘yan kasuwa na MOMAN sun bi wannan umarni, kuma sun canza farashin litar su kamar yadd aka yi umarni.

Takarda ba ta zo mana ba - IPMAN

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa takardar da gwamnati ta fitar a game da karin farashin ya shiga hannun kungiyoyin MOMAN da kuma IPMAN.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da karin da aka yi, kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan da ke dakon man fetur a Najeriya ta nuna abin bai yi mata, za ta so a kara daga farashin.

Fetur
Gidan mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaban IPMAN na kasa, Chinedu Okonkwo ya shaidawa Vanguard cewa labari ya zo gare su a game da karin farashin, amma takardar ba ta iso ba.

Mista Chinedu Okonkwo yake cewa a halin da ake, ba za su iya daukar mataki ba sai sun samu sanarwa a hukumance daga gwamnatin tarayya tukun.

Kara karanta wannan

Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock

Kungiyar ‘yan kasuwan ta IPMAN ta ce a halin yanzu fetur ya yi wahala sosai, amma ana sa rai tun da an kara farashin, hakan ya yi maganin karancin.

Mike Osatuyi wanda yana cikin shugabannin IPMAN a Najeriya, ya bayyana cewa a kan N240 ake saida masu litar man fetur a manyan tashoshin kasar.

Business Day ta ce ana haka ne sai aka ji gwamnatin Muhammadu Buhari ta na jaddada cewa za ta janye tallafin man fetur a cikin farkon shekarar nan.

Gwamnoni za su hadu da Gwamnan CBN

A baya an samu labari Kungiyar gwamnonin jihohi 36 za ta zauna da Godwin Emefiele domin jin hikimar tsare-tsaren da ya kawo a Najeriya.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar da sanarwar wannan taro da aka yi a makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel