Kamar wasa, Ministan Buhari Ya Kai Karar EFCC, ICPC a Kotu a kan Bidiyon Atiku

Kamar wasa, Ministan Buhari Ya Kai Karar EFCC, ICPC a Kotu a kan Bidiyon Atiku

Wa’adin bukatar da Festus Keyamo SAN ya kai gaban EFCC da ICPC ya cika a cikin makon nan

Ministan ya shigar da korafi kan Atiku Abubakar mai takarar kujerar shugaban kasa a 2023

Kakakin kwamitin APC-PCC ya garzaya kotu, yana so ayi umarni da bincike a kan ‘Dan takaran

Abuja - Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Festus Keyamo, ya shigar da kara a kan hukumomin EFCC, ICPC da CCB.

Daily Trust ta ce Festus Keyamo SAN yana karar hukumar EFCC, yana neman a tursasa mata yin bincike a kan ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.

Lauyan ya hada da hukumomin ICPC da CCB a karar da ya shigar, ganin cewa wa’adin sa’o’o 72 da ya bada domin a binciki ‘dan takaran ya shude.

Kara karanta wannan

Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

Ministan kwadagon ya na so a cafke tsohon mataimakin shgaban na Najeriya, kuma a bincike shi a kan zargin aikta laifuffukan da suka sabawa doka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zargin da suke kan Atiku

Keyamo yana tuhumar Atiku Abubakar da sabawa dokar CCB da na aikin gwamnati, da kin bin dokar safarar kudi da aikata laifin cin amana da sata.

Rahoton ya ce Lauyan ya je kotu ne a sanadiyyar wasu bidiyo da tsohon hadimin ‘dan takarar, Mr. Michael Achimugu ya fitar a kan ‘dan takaran PDP.

Atiku
Ana yi wa Atiku Abubakar kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Ana zargin an ji Wazirin Adamawa yana bayanin yadda suke take doka wajen cin karensu babu babbaka a lokacin gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo.

Bukatar da Keyamo ya kai wa Alkali

Rokon da Keyamo yake yi shi ne babban kotun tarayya mai zama a Abuja, ta tilastawa hukumomin yaki da rashin gaskiya binciken ‘dan siyasar.

Kara karanta wannan

Shekaru 30 da Rushe Zabe, Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Hana a Mikawa Abiola Mulki

Vanguard ta ce Darektan kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu yana so Atiku ya gabatar da kan shi a gaban hukuma domin a ji dadin bincikensa.

Baya ga haka, karamin Ministan yana so Alkali ya zartar da cewa dole sauran wadanda ake tuhuma da zargin aikata ba daidai ba, su mika kansu.

Wanda ya shigar da karar yana ganin cewa Michael Achimugu ya fallasa tsohon mataimakin shugaban kasar, don haka akwai bukatar doka tayi aiki.

Matsayar Limaman Katolika

Ganin zaben 2023 ya karaso gadan-gadan, an samu labari cewa jagororin limaman cocin katolika sun ba mabiyansu satar amsa kan wanda za a zaba.

Malaman addinin kiristan na yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun kira taro a Ibadan., suka ce a zabi wanda ba zai yi wa mutane rashin adalci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel