Rikicin PDP: Kar ku zargi G-5 idan aka gaza samun masalaha kafin zabe, Ortom

Rikicin PDP: Kar ku zargi G-5 idan aka gaza samun masalaha kafin zabe, Ortom

  • Gwamna Ortom ya ce shugabannin PDP su zargi kansu idan har tattaunar neman sulhu da G-5 ta rushe
  • Gwamnan jihar Benuwai yace gwamnonin G5 sun ba da isasshen lokaci da dama ga bangaren shugabancin PDP
  • Ortom ya bayyana dan takarar shugaban kasan da a tunaninsa ya dace da Najeriya a wannan halin

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce shugabancin jam'iyar PDP karƙashin Dakta Iyorchia Ayu, kar su zargi kowa sai kansu idan har zaman sulhu da gwamnonin G-5 ya rushe.

Gwamnan ya bayyana cewa girman kai, jiji da kai da son mulki daga ɓangaren shugabannin PDP ne ke kawo tsaiko a kokarin lalubo masalaha kan sabanin da ya raba jam'iyya gida biyu.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
Rikicin PDP: Kar ku zargi G-5 idan aka gaza samun masalaha kafin zabe, Ortom Hoto: vanguardngr
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Ortom, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar gwamnonin G-5 ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Taron kamfen da rikicin PDP: Gwamnan PDP ba zai marabci Atiku a jiharsa ba bisa dalilai

Ya yi bayanin cewa saɓanin yadda ake raɗe-raɗi gwamnonin G-5 ba su rasa madafa ba amma su mutane ne masu kauna da biyayya ga jam'iyyar PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Ortom, tawagar G-5 ta ba da isasshen lokaci domin a samu maslaha da fahimtar juna ta gaske kuma mai dorewa domin a ceto jam'iyyar da suka jagoranci gina wa daga rugujewa.

A ruwayar Punchi, Ortom ya ce:

"Ina ganin muna kan hanya a iya sanina game da tawagarmu, mutane ne masu biyayya ga jam'iyya, mun ba da isasshen lokaci. An faɗa mana jagororin PDP zasu yi duk me yuwuwa su shawo kan lamarin."
"Akwai hanyoyi da dama na magance batutuwa irin wannan ko da kuwa ba zaka iya cika buƙatun tawaga ko daidaikun mutane ba, kai zaka lalubo hanyar zama."

Peter Obi ya cancanci zama shugaban kasa - Ortom

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

Da yake tsokaci kan takarar shugaban kasan da ya kwanta masa, Ortom ya ce da ba'a a PDP yake ba, da yana gaba-gaba a yakin neman zaben Peter Obi na Labour Party.

A cewar gwamnan, Obi kamar kowane ɗan Adam tara yake bai cika 10 ba amma yana da gogewar shugaban da Najeriya take bukata a halin da take ciki a yanzu.

A wani labarin kuma Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Jirgin dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ya dira Ibadan, jihar Oyo amma an nemi gwamnan jihar an rasa tun a filin jirgi.

Gwamna Makinde na ɗaya daga cikin gwamnonin G5 masu fushi da PDP kuma shi ne ɗan takarar gwamna a 2023 a inuwar jam'iyyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel