Shugaban Najeriya Buhari Ya Zauna da Emefiele Bayan Gwamnan CBN Ya Koma Aiki

Shugaban Najeriya Buhari Ya Zauna da Emefiele Bayan Gwamnan CBN Ya Koma Aiki

  • A yau aka tabbatar da cewa Godwin Emefiele ya shiga fadar shugaban Najeriya da ke birnin Abuja
  • Gwamnan babban bankin kasar na CBN ya samu damar sa labule tare da Muhammadu Buhari
  • Emefiele yana cikin ‘yan rakiyar shugaban bankin BADEA dazu kafin ya zauna da shugaban kasar

Abuja - Yanzu haka da muke tattara rahoton, labari yana zuwa mana cewa Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele yana cikin fadar Aso Rock.

Punch ta kawo rahoto dazu cewa Mista Godwin Emefiele ya shiga fadar shugaban kasa, kuma ya samu damar haduwa da Muhammadu Buhari.

Zuwa yanzu, Legit.ng ba ta da masaniyar abin da wannan zama da ake yi ya kunsa, sai dai watakila bai rasa nasaba da abubuwan da ke faruwa.

A kwanakin nan an taso Godwin Emefiele a gaba da zargin taimakawa ta’addanci, kuma ana sukar tsarin da ya kawo na takaita yawon kudi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Zama na biyu da aka yi da Gwamnan CBN

Jaridar ta ce wannan ne karo na biyu da gwamnan babban bankin kasar ya hadu da Mai girma shugaban kasa tun bayan dawowarsa Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An fahimci cewa kafin nan, Emefiele yana cikin tawagar da tayi wa Dr Sidi Ould Tah zuwa fadar shugaban Najeriya a safiyar Alhamis dinnan.

Shugaban Najeriya
Tawagar Dr Sidi Ould Tah a Aso Villa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A matsayinsa Darekta Janar na babban bankin Larabawa na BADEA da aka kafa domin cigaban tattalin arziki ya yi zama da shugaban Najeriya.

Daya daga cikin hadiman shugaban Najeriya, Bashir Ahmaad ya tabbatar da cewa mai gidansa ya hadu da ‘yan tawagar Dr. Sidi Ould Tah a Abuja.

Bayan nan sai labari ya zo cewa gwamnan ya kebe da Muhammadu Buhari, wannan karo shi kadai ba tare da su Gwamna Babagana U. Zulum ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Iso Abuja Daga Kasar Mauritania

Buhari da Emefiele sun hadu a Daura

Bayan bankin CBN ya bada sanarwar canza manyan takardun kudi, Emefiele ya je garin Daura, ya yi wa shugaban kasa karin bayani kan lamarin.

Baya ga zaman da aka yi a Daura, rahoton yace gwamnan na CBN da yake fuskantar barazanar jami’an DSS ya yi wani zama da Buhari a ofishinsa.

Aikin NDLEA yana kyau

Ku na da labarin yadda jagorancin Buba Marwa ya jawo NDLEA ta cafke mutane 26, 458 a shekaru biyu bisa zargin safara da harkar miyagun kwayoyi.

Janar Marwa ya ce sun yi ram da manyan ‘yan kwaya 34, kuma an karbe dukiyar da suka tara, don haka ya gargadi masu harkar kwaya su sake tunani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel