Shekaru 24 na Kura-Kurai, Rashin Zabi Nagari ne Suka Kawo Najeriya inda Take, Kwankwaso

Shekaru 24 na Kura-Kurai, Rashin Zabi Nagari ne Suka Kawo Najeriya inda Take, Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, 'dan takarar kujerar shugabancin kasa na NNPP a Najeriya yace kura-kuran shekaru 24 ke bibiyar Najeriya
  • Ya bayyana a gaban gidan Chatham a Landan inda ya sanar da cewa rasin zabin shugabanni nagari ne suka tsunduma Najeriya cikin halin da ta ke ciki
  • Kwankwaso yace ganin cewa ya nakalci dukkan abubuwan da suka addabi Najeriya, shiyasa yake ganin shi yafi dacewa ya jagoranci kasar

Abinda Najeriya ke fuskanta a halin yanzu tattaruwar kura-kuran shugabanci da rashin zabin nagari ne da aka kwashe sama da shekaru ashirin ana yi, kamar yadda 'dan takarar shugabacin kasan na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar, Daily Trust ta rahoto.

Rabiu Musa Kwankwaso
Shekaru 24 na Kura-Kurai, Rashin Zabi Nagari ne Suka Kawo Najeriya inda Take, Kwankwaso. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Tsohon ministan tsaron ya bayyana matsayarsa yayin da ya ke jawabi ga Gidan Chatham da ke Landan inda yayi magana kan zaben 2023 mai gabatowa, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Wike Ya Yi Sabuwar Magana Kan Wanda Zai Goyi Baya a 2023

"Za mu iya nuna dukkan wasu nau'ikan abubuwan da muke zargin sun saka mu a wannan hali, daga annobar korona zuwa karayar tattalin arziki, daga ikon yamma zuwa jarin kasashe, da sauransu."

- Kwankwaso yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Amma a wurina, muna inda mu ke ne saboda kura-kuran da rashin zabi nagari na jama'armu wadanda suka damka amanar shugabancin Najeriya inda bai dace ba a shekaru 24 da suka gabata."

Kwankwaso wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne ya bayyana manyan kalubalen da yace kasar nan na fuskanta a yau kamar, rashin tsaro, karuwar talauci, karuwa da rashin daidaita farashin kayayyaki, cigaban rashin aikin yi da dogaro, lalacewar ababen more rayuwa tare da yawan mutuwar mata wurin haihuwa da jariransu.

Sauran lamurran da ya lissafo sun hada da lalacewar bangaren ilimi, matsala a bangaren lafiya, karuwar rashawa, satar man fetur na fitar hankali da suaran ma'adanai tare da rashin yarda a tsakanin al'ummar kasar mu.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC Sun Damke Mai POS da 'Yan Bindiga Suka Girke Yana Musu Hada-hadar Kudi

Kwankwaso yace yana fatan zama shugaban kasan Najeriya na gaba saboda:

"Na fahimci matsalolin da mu ke da su, kura-kuran da aka tafka, abubuwan da basu dace ba aka basu fifiko kuma tare da tawagarmu, za mu tabbatar da mu cimma burika da fatan 'yan Najeriya."

Ya kara da cewa:

"Mun fahimta, mu yarda da tare da fama da takaicin. Kuma mun hada tsarin da zai shawo kan kowanne irin kalubalen da ke addabar kasarmu."

Za a yi zaben 2023, babu dagewa ko fasa, FG

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta jaddada cewa za a yi zaben 2023 mai gabatowa.

Tace a shirya ta ke kuma jami'an tsaro sun kammala shiryawa don haka babu gudu babu ja da baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel