Akwai Banbanci Sosai: Budurwa Ta Saki Bidiyon Yadda Ta Sauya Cikin Watanni 3 Da Komawarta UK

Akwai Banbanci Sosai: Budurwa Ta Saki Bidiyon Yadda Ta Sauya Cikin Watanni 3 Da Komawarta UK

  • Wata mutuniyar kasar Ghana ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta baje kolin sauyawar da ta yi bayan ta shafe watanni uku a kasar Birtaniya
  • A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta, ta kuma bayyana yadda kamanninta suke a da bayan shafe shekaru 25 a Ghana
  • A cewarta, komawarta Turai shawara ce mai kyau kuma tana farin ciki da komawa sabon wuri da zama

Wata matashiyar budurwa mai suna @afrapapabi a TikTok ta wallafa wani hadadden bidiyo na sauyawar da ta yi bayan ta koma kasar Birtaniya da zama.

A wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, ta kwatanta sauyawar da ta yi da kuma yadda kamanninta suke a baya bayan ta shafe tsawon shekaru 25 a kasar Ghana.

Budurwa
Akwai Banbanci Sosai: Budurwa Ta Saki Bidiyon Yadda Ta Sauya Cikin Watanni 3 Da Komawarta UK Hoto: @afrapapabi/TikTok
Asali: UGC

A cewarta, sauyawar da ta yi ya faru ne a cikin watanni uku bayan ta yanke shawarar komawa UK.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: DPO ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, Ta Rasu a Take

Da take wallafa bidiyon, ta bayyana cewa duk wanda ya ce zuwa Turai babu dadi toh ba gaskiya yake fadi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta rubuta:

"Wa ya ce Turai bai yi ba? shekaru 25 a Ghana da watanni 3 a UK."

Jama'a sun yi martani

@Bellz ta yo martani:

"Tun dama chan ke mai kyau ce, banbancin kawai kamarar ce."

@Usher Raymond Dawson ya yi martani:

"Ban san ki ba amma wannan shine abu mafi kyau da za ki yi. Kada ki yi mafarkin dawowa nan. Addo na gasa yan maza."

@Thessy ta rubuta:

"Hatta iskan UK na iya sauya kamannin mutum gaba daya."

@Esinam ta ce:

"Yarinya irin sauyin da nake magana a kai kenan. Mashaa Allah. Kada ki yi mafarkin dawowa nan dan Allah."

@Amon Treasure Jahday ta kara a da cewar:

"Idan kana bukatar karamar yarinya don taimakawa da aikin gida ina nan zan tura takarda a lokaci daya."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Yan Najeriya sun cika da mamaki bayan ganin mai kama da Shugaba Buhari yana yawo

A wani labari na daban, jama'a sun cika da mamaki bayan cin karo da wani mai kama da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tafiya a kan titi.

Mutumin wanda jama'a suka kewaye ya dungi karfafawa matasan Najeriya gwiwa kan cewa sune yara manyan gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng