DPO Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, a Take Ya Sheka Lahira

DPO Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, a Take Ya Sheka Lahira

  • Mutane da dama sun kadu da jin yadda wani DPO marabar Seme da ke jihar Legas, SP Mojeed Salami ya yanke jiki ya fadi tare da mutuwa a ofishinsa ranar Talata
  • Duk da ba a gama gono musabbabin mutuwarsa ba, sai dai wata majiyar 'yan sandan ta bayyana yadda yayi korafi game da wani dan ciwon kai har ya je asibiti ya dawo
  • Bayan wasu awanni ya kira yaronsa na wurin aiki ya umarcesa da ya kira masa DCO, koda ya dawo sai ya iskeshi a kasa warwas yana numfashi sama-sama

Legas - DPO marabar Seme da ke jihar Legas, SP Mojeed Salami, ya yanke jiki ya mutu a ofishinsa ranar Talata, Daily Trust ta rahoto hakan.

Mataccen DPO
DPO Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, a Take Ya Sheka Lahira. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da har yanzu ba a san musabbabin mutuwar tasa ba, sai dai wata majiyar 'yan sandan da ta zanta da manema labarai jiya ya bayyana yadda DPO a baya yabke korafi game da 'dan wani ciwon kai da yake fama da shi, kuma har ya je asibiti.

Kara karanta wannan

Shekaru 15 Bayan Barin Mulki, Obasanjo Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Yin Tazarce Sau 2

Daily Trust ta rahoto cewa, kamar yadda ya bayyana, DPO ya dawo daga ofishinsa bayan wasu awanni kuma ya koma kan aikinsa, sai dai bayan wasu awanni ya kira yaronsa na wurin aiki gami da shaida musu yana jinsa wani iri.

A cewar majiyar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ya bukaci yaronsa ya kira DCO din shi. Ina ga ya so mikawa DCO ragamar aikin ne.
"Yaron nasa ya iske shi a kasa yana numfashi sama-sama. An garzaya da shi babban asibitin Badagry inda aka tabbatar da mutuwarsa."

Kakakin 'yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce:

"Ya rasu ranar Talata. Hakan ya ba kowa mamaki saboda babu wani abu babba game da mutuwarsa. Sun san kawai yayi korafi game da wani 'dan ciwon kai, ya je asibitin, ya dawo, kuma ya koma kan aiki daga bisani ya rasu."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Rikicin manoma da makiyaya yayi ajalin rai daya

A wani labari na daban, arangama tsakanin makiyaya da manoma a wani yanki na jihar Kwara yayi ajalin ran manomi guda daya.

Lamarin ya ritsa da wasu inda har aka kone gidaje sama da 500 a yankunan da tarzoman ta tashi a jihar arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel