Za a Fara Hako Man Fetur a Jihar Nasarawa a Watan Maris Mai Zuwa, Mele Kyari

Za a Fara Hako Man Fetur a Jihar Nasarawa a Watan Maris Mai Zuwa, Mele Kyari

  • Babban manajan daraktan matatar man fetur ta kasa, Mele Kyari, yace a hukumance za a fara hako man fetur daga rijiyar farko ta jihar Nasarawa a watan Maris
  • Kyari ya bayyana hakan ne a wata ziyara da 'yan asalin jihar suka kai masa karkashin jagorancin Gwamna Sule Abdullahi na jihar
  • Yayi kira ga al'ummar jihar da su bayar da hadin kai tare da muhallin hakar fetur din ba tare da hatsaniya ba kamar yadda ake samu a Neja Delta

FCT, Abuja - Matatar man fetur ta kasa tace a hukumance za a fara hako rijiyar man fetur ta kasa a jihar Nasarawa a watan Maris din 2023, jaridar TheCable ta rahoto.

Mele Kyari da Sule Abdullahi
Za a Fara Hako Man Fetur a Jihar Nasarawa a Watan Maris Mai Zuwa, Mele Kyari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Mele Kyari, GCEO din NNPC ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ziyarar da wakilan jihar Nasarawa da suka samu jagorancin Gwamna Abdullahi Sule suka kai masa.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Kyari yace wannan ganowar ya na daga cikin cigaba da hako man fetur da ake yi a tudu a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Dole a yi aikin nan da hanzari saboda duniya yanzu ta fara gujewa kayayyakin nan fetur saboda sauyin makamashi da ake samu, idan ka shiga kasuwar da wuri, hakan zai fi.”

- Kyari yace.

“Idan ba haka ba, nan da shekaru 10 babu wanda zai amince ya narka kudinsa a kasuwancin man fetur sai dai kuma idan daga kudin ka zai fito.”

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, ya kara da cewa, goyon bayan al’umma da kuma muhalli su ne muhimman abubuwan da za su da aiki a yankin a samu nasara don gujewa abinda ya faru a Niger Delta.

A wata takarda, NNPC tace tana tsammanin kara samun man fetur din a wasu yankunan Arewacin Najeriya da suka hada da Nasarawa, bayan samunsa da tayi a Bauchi da Gombe.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Baya ga arewa, an lissafa jihar Anambra matsayin wani yanki da NNPC ke kokarin gano nan fetur.

Buhari ya kaddamar da hakar mai a rijiyar Kolmani, karo na farko a arewa

A wani labari na daban, a karshen shekarar da ta gabata ta 2022 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hakar maI a rijiyar Kolmani da ke tsakankanin jihohin Gombe da Bauchi a arewa.

Gagagrumin bikin ya samu halartar manyan jiga-jigan kasar nan da suka ministoci da gwamnonin jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel